Jimillar Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Kai N121tr, an Fadi Dalilin Karuwarsa

Jimillar Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Kai N121tr, an Fadi Dalilin Karuwarsa

  • A cikin watanni uku na farkon shekarar 2024, Najeriya ta ciyo sabon bashin zunzurutun kuɗi har Naira tiriliyan 7.7
  • Ofishin kula da basussuka (DMO) ne ya bayyana kan a cikin wata sanarwa kan jimillar basussukan da ake bin ƙasar nan
  • DMO ya yi bayanin cewa basussukan da aka biyo Najeriya sun ƙaru daga N97.34tr a watanni uku na ƙarshen 2023 zuwa N121.67tr a watanni uku na farkon 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ofishin kula da basussuka (DMO) ya bayyana bashin da ƙasar nan ta ciwo a cikin watanni uku na farkon shekarar 2024.

Ofishin ya fayyace cewa sabon bashin da Najeriya ta ciyo ya kai N7.71tr a watanni uku na farkon wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Emefiele: Bayan ƙwace kadarorin N12bn, tsohon gwamnan CBN ya nemi alfarma a kotu

Najeriya ta ciyo bashin N7.7tr
Najeriya ta ciyo bashin N7.7tr a wata uku na farkon 2024 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin na DMO ya fitar a ranar Laraba, wacce ya sanya a shafinsa na yanar gizo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DMO ya yi bayanin cewa sabon bashin ya haɗa da N2.81tr na ɓangaren bashin cikin gida na N6.06tr da ke cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.

Sannan sai N4.90tr da aka yi amfani da shi wajen samun bashin N7.3tr na 'Ways and Means' wanda majalisar tarayya ta amince da shi.

Ofishin ya nuna cewa ƙarin da aka samu na N24.33tr a bashin da ke bin ƙasar nan, ya samu ne saboda sabon rancen da aka karɓo da kuma karya darajar Naira.

Meyasa bashin Najeriya ya ƙaru?

DMO ya yi nuni da cewa farashin Dala ya tashi daga N899.39/$1 a watanni uku na ƙarshen shekarar 2023 zuwa N1,330.26/$1 a watanni uku na farkon shekarar 2024, wanda hakan ya sanya basussukan waje da ake bin ƙasar nan suka ƙaru a farashin Naira.

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

A watanni uku na farkon 2024, jimillar basussukan da ake bin ƙasar nan ya kai N121.67tr, daga N97.34tr da yake a watanni uku na ƙarshen 2023.

DMO ya yi bayanin cewa yayin da jimillar basussukan waje da ake bin ƙasar nan yana nan yadda yake a Dala, ƙarin da aka samu na yawansa a Naira ya faru ne sakamakon karya darajar Naira.

Hakan na nufin tun da kusan N7.71tr sabon bashi ne, kusan ƙarin N16.62tr da aka samu ya faru ne saboda karya darajar Naira.

CBN ya dakatar da ba gwamnati bashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu ya daina bayar da bashin 'Ways and Means' ga gwamnatin tarayyar Najeriya.

Gwamnan babban bankin na CBN, Olayemi Cardoso, ya ce ya dauki matakin ne saboda gazawar gwamnati wajen biyan basussukan da ake bin ta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng