Limami Ya Shiga Matsala Kan Zuwa Aikin Hajji Babu Izinin Basarake, an Yi Masa Barazana
- Babban limamin masallacin Juma'a ya shiga matsala a jihar Oyo bayan tafiya aikin hajji ba tare da izinin Sarkinsa ba
- Sarkin Ogbomosho, Oba Afolabi Ghandi ya kalubalanci limamin inda ya ce ya saba ka'idar da suka yi kafin nada shi mukamin
- Basaraken ya ce limamin ya sanya hannu a yarjejeniya kafin nada shi mukamin wanda aka gindaya masa wasu sharuda
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Mai sarautar Ogbomos da ke jihar Oyo, Oba Afolabi Ghandi ya nuna bacin ransa kan yadda babban limami ya saba dokarsa a yankin.
Basaraken ya caccaki babban limamin mai suna Sheikh Taliat Yunus Olusina kan tafiya aikin hajji ba tare da izininsa ba.
Basarake ya fusata da halin babban limami
Vanguard ta ruwaito cewa basaraken ya dade yana takun saka da limamin tsawon lokaci kafin wannan matsalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Basaraken a cikin takardar zargin, ya ce limamin bai nemi izni ba kafin wucewa aikin hajji a Saudiyya a karan kansa.
Ya ce daukar wannan mataki na limamin ya saba yarjejeniyar da suka yi kafin a ba shi mukamin babban limami, cewar Daily Post.
Takardar da Sarki ya rubutawa limami
"Ina mai rubuta korafi a gare ka saboda wasu halaye da kake nunawa a matsayinka na limamin Ogbomoso, ya kamata ka bar irin wadannan halaye."
"Idan ba ka manta ba, kafin nada ka babban limami ka sanya hannun kan yarjejeniya da dokokin da aka gindaya maka."
"A cikin yarjejeniyar, ka sanya hannu cewa zaka sanar da sarkin Ogbomoso kafin barin kasar Najeriya zuwa wani wuri."
- Sarki Afolabi Ghandi
Korafin basarake kan babban limami a Oyo
Basaraken har ila yau, ya kalubalanci sarkin kan nada magajinsa wanda ya jagoranci sallar Juma'a bayan tafiyarsa.
Ya ce hakan ya saba ka'idar da suka yi na cewa ba zai yi haka ba har sai da saninsa wanda ya ce dole ya zo ya amsa tambayoyi.
A martaninsa, babban limamin ya tabbatar da haka inda ya wannan ba shi ne karon farko da ya ke rubuta takarda kansa ba.
Malamin Musulunci ya shawarci 'yan siyasa
Kun ji cewa malamin Musulunci, Sheikh Muhydeen Bello ya bayyana 'yan siyasa a matsayin marasa tsoron Allah.
Shehin malamin ya shawarce su da su aikawar da ayyukan alheri lokacin da suke mulki kafin damar ta subuce musu daga baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng