Gwamnan Kano Ya Ware N4.8bn Domin Gyara Makarantu, Mutane 17, 000 Za Su Samu Aiki
- Gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware makudan kudi domin yin ayyuka na musamman a ɓangare ilimi
- Rahotanni sun nuna cewa ayyukan za su shafi dukkan kananan hukumomin jihar guda 44 domin inganta ilimin karkara da birni
- Daraktan yada labaran gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya yi karin haske kan ayyukan da ma'aikata da za a dauka a jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ware makudan kudi domin haɓaka ilimi a dukkan fadin jihar.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa manyan ayyukan za su shafi dukkan sassan jihar ciki har da ƙauyuka.
Legit ta gano haka ne cikin wani sako da daraktan yada labaran gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: Za a gyara makarantun firamare
Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya tabbatar da cewa gwamnatin ta ware N1.9b domin gyare-gyaren makarantun firamare a jihar.
Ya kuma kara da cewa kwaskwarimar za ta shafi dukkan makarantun firamare da suke kananan hukumomin jihar guda 44.
Za a gina sababbin ajujuwa a Kano
Har ila yau, Abba Kabir Yusuf ya ware kudi kimanin N2.9b domin gina ajujuwa a fadin jihar, rahoton Daily Trust.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya ce za a yi amfani da kuɗin ne domin gina ajujuwa a makarantun firamare saboda inganta ilimi daga tushe.
Za a dauki ma'aikata a makarantun Kano
Har ila yau, gwamantin ta tabbatar da cewa za a ɗauki masu gadi 17,600 a makarantun jihar domin inganta tsaro.
An bayyana cewa kowace karamar hukuma a jihar Kano za ta samu masu gadi 400 domin kare makarantun jihar.
Gwamnatin Kano ta soke lasisin makarantu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya soke lasisin makarantu masu zaman kansu gaba daya a jihar kwanaki.
Wannan na daga cikin matakin da gwamnati ke yi na tabbatar da makarantun sun cike tsari da ka'idoji domin samun ilimi mai inganci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng