'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Ta'addan IPOB a Jihar Ebonyi

'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Ta'addan IPOB a Jihar Ebonyi

  • Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan ta'addan IPOB suka kai a wani ofishin ƴan sanda
  • Ƴan sandan sun hallaka ƴan ta'addan mutum biyar bayan sun kwashe dogon lokaci sun musayar wuta a daren ranar Laraba
  • Ƴan ta'addan dai sun farmaki ofishin ƴan sandan ne na Ishieke da misalin ƙarfe 9:30 na daren ranar Laraba, 26 ga watan Yunin 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ebonyi - Jami'an ƴan sanda sun hallaka ƴan ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) mutum biyar a ƙaramar hukumar Ebonyi ta jihar Ebonyi.

Jami'an ƴan sandan sun hallaka masu tayar da ƙayar bayan ne a yayin wani artabu da suka yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro, sun sace mutum 20 a Kaduna

'Yan sanda sun hallaka 'yan ta'addan IPOB a Ebonyi
'Yan sanda sun sheke 'yan ta'addan IPOB a jihar Ebonyi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Ƴan IPOB sun farmaki ofishin ƴan sanda

Ƴan ƙungiyar ta IPOB sun kai farmaki ofishin ƴan sanda na Ishieke a cikin wata motar bas ƙirar Sienna mai launin shuɗi da misalin ƙarfe 9:30.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne a daren Laraba inda miyagun suka buɗe wuta kan ofishin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Sai dai ƴan sanda sun ci ƙarfinsu a wani artabu da ya ɗauki tsawon mintuna 30 ana fafatawa.

Artaban tsagerun IPOB da jami'an tsaro

Hakazalika, jami’ai daga hedkwatar rundunar ƴan sandan jihar da ke Abakaliki da sojoji sun yi gaggawar kawo ɗauki bayan samun kiran gaggawa daga ofishin ƴan sandan na Ishieke.

Wata majiya mai tushe ta ce harbe-harben da aka yi ya tilastawa mazauna garin tserewa domin tsira da rayukansu.

"Ƴan bindigan sun je ofishin ƴan sanda na Ishieke sannan suka buɗe wuta. Ƴan sanda sun mayar da martani inda aka kwashe kusan tsawon mintuna 30, kafin sauran jami'an tsaro su iso wajen."

Kara karanta wannan

El Rufai, Ministan Tinubu da wasu ƴan Najeriya da suka mallaki gidajen alfarman N1.49trn a Dubai

"Jami'an tsaro da dama ciki har da sojoji sun zo domin tunkarar ƴan ta'addan."

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan harin IPOB?

Rundunar ƴan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan aukuwar lamarin.

Ko da wakilin Legit Hausa ya tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi, ASP Ukandu Joshua, domin samun ƙarin bayani, ya bayyana cewa a jira shi zai kira daga baya.

"Eh ina wani abu a yanzu ka jira zan kira ka daga baya."

- ASP Ukandu Joshua

Sai dai, bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan sanda sun cafke ɓarawo

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wani babban ɓarawo mai suna Glory Samuel wanda ya ƙware wajen ɗauke-ɗauke.

Rundunar yan sanda tana zargin Glory Samuel da hannu a satar maƙudan kuɗaɗe da kayayyakin mutane da dama a jihar da ke yankin Arewa maso Gabas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel