“Kamar Kowa Kake a Yanzu”: Abba Kabir Ya Fayyace Matsayin Aminu Ado a Kano

“Kamar Kowa Kake a Yanzu”: Abba Kabir Ya Fayyace Matsayin Aminu Ado a Kano

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, Gwamnatin jihar ta yi magana kan yadda take ganin Aminu Ado
  • Gwamnatin ta ce tun bayan daukar matakin Majalisar jihar da kotu, Aminu Ado ya dawo kamar sauran 'yan jihar
  • Kakakin gwamnan jihar, Sanusi Bature ya bayyana haka inda ya ce wasu 'yan siyasa ne suke zuga Aminu Ado

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya sake magana kan makomar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce a yanzu Aminu Ado Bayero darajarsa kamar sauran 'yan jihar ne ba tare da wani bambanci ba.

Abba Kabir ya magantu kan matsayin Aminu Ado a Kano
Gwamna Abba Kabir ya ce a yanzu Aminu Ado kamar kowa yake a Kano. Hoto: Sanusi II, Abba Kabir Yusuf, Masarautar Kano.
Asali: UGC

Abba ya magantu kan matsayin Aminu Ado

Kara karanta wannan

"Ban san Aminu Ado ba": Kwamishinan 'yan sanda ya fadi matsayarsa kan rigimar Kano

Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana haka a jiya Laraba 26 ga watan Yunin 2024 a birnin Kano, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dawakin Tofa ya ce hukucin Babbar Kotun jihar ya tabbatar da matakin Majalisar na mayar da Aminu Ado kamar sauran jama'a a jihar, Daily Post ta tattaro.

"Matakin Majalisar jihar Kano ya tabbata bayan hukuncin kotu, Aminu Ado yanzu kamar sauran 'yan jihar kano ya ke."
"Bai kamata ya rika mamaye wuraren gwamnati ba, inda ya ke zaune na laka ne wanda ya tilasta kansa zama a can."

- Sanusi Bature Dawakin Tofa

Abba ya gano masu zuga Aminu Ado

Bature har ila yau, ya zargi wasu 'yan siyasa da zuga Aminu Ado domin ya ci gaba da fafatwa domin neman sarauta.

Ya bayyana cewa lokacin da aka tube Sanusi II babu wani mataki da ya dauka kan gwamnatin da ta shude.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya ceto iyalin Sarki Ado Bayero da ake neman tozartawa a gidan haya

'Yan sanda sun karyata alaka da Aminu Ado

A wani labarin, kun ji cewa kwamishinan 'yan sanda a jihar kano, Salman Garba ya musanta wata alaka da Aminun Ado Bayero.

Salman yana magana ne bayan zargin cewa suna da alaka ta jini da tsohon sarkin wanda mahaifiyarsa ta fito daga jihar Kwara.

Garba ya ce ya zo Kano ne domin yin aiki tukuru da dakile matsalolinta ba wai kare muradun wasu tsiraru a jihar ba musamman kan rigimar sarauta a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.