Jihohi 3 da ke Zargin Gwamnatin Tarayya da Yi Masu Katsalandan

Jihohi 3 da ke Zargin Gwamnatin Tarayya da Yi Masu Katsalandan

Ana ci gaba da kokarin warware wasu daga matsalolin Najeriya, sai dai akwai jihohin da ke ganin gwamnatin tarayya na shiga ayyukansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Matsalar da jihohin su ka samu ya samo asali ne daga rigingimu da wadanda suka yi mulki a baya.

A wanna labarin, mun dauki jihohi uku a Najeriya da ke zargin gwamnatin tarayya na shiga yada su ke tafiyar da al'amuransu.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

1. Jihar Kano

Rikicin jihar Kano asali ya samo daga rashin jituwa da aka samu tsakanin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

A shekarar 2016 ne rikicin Kwankwaso da Ganduje ya kara zafi bayan ziyarar ta'azziyar mahaifiyar Ganduje.

Kara karanta wannan

Rikicin manoma da makiyaya ya jawo an kashe mutane da dama a Jigawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin
Jihohin sun samu matsala ne da tsofaffin gwamnoninsu Hoto: Abba Kabir Yusuf/Dauda Lawal/Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa APC ta zargi Kwankwaso da nuna rashin da'a tare da dauko hayar yan daba su na raba fastoci dauke da rubutun 'Kwankwaso 2019.'

Haka dai aka yi ta saboda rikice rikicen siyasa har Abdullahi Ganduje ya zama shugaban jam'iyyar APC, NNPP wacce Rabi'u Musa Kwankwaso ke zama kusa a cikinta na mulkin Kano.

Zargin gwamnatin tarayya da katsalandan a Kano

Wasu daga manya-manyan abubuwan da ake zargin gwamnatin tarayya na katsalandan a Kano sun hada da;

1. Dawo da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero bayan gwamnati ta tsige shi

2. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taba zargin jami'an tsaro na bijirewa umarnin da ya ke basu saboda su na karbar umarni daga 'sama.'

3. Samarwa Sarki Ado Bayero jami'an tsaro masu ba shi kariya

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

4. Zargin ofishin mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro da hannu dumu-dumu cikin rikicin masarauta, duk da an janye wannan daga baya

Har yanzu ta na kasa ta na dabo, yayin da ake jiran hukuncin kotu kan dambarwar masarauta a Kano.

2.Jihar Zamfara

A jihar Zamfara, matsalar da ake samu ta biyo bayan rashin jituwa da tsohon gwamna kuma karamin ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle da gwamnan PDP a jihar, Dauda Lawal.

Gwamnatin Zamfara na zargin tsohon gwamnan da hannu cikin cin hanci da ake zargin tsohuwar gwamnatinsa da aikatawa.

Rikicin gwamnatin Zamfara da gwamnatin tarayya

1. Zargin Bello Matawalle da wawashe kudin jama'a kamar yadda BBC ta wallafa

2. Zargin karamin ministan tsaro da raba kayan abinci ga yan bindiga, lamarin da APC ta ce sharri ne

3. Zargin da gwamna Dauda Lawal ke yi na cewa gwamnatin tarayya na gaban kanta wajen shiga yarjejeniyar sulhu da 'yan ta'adda

Kara karanta wannan

"Mutanen Kano ba su goyon bayan rushe sarakuna da maido Sanusi II," Dan'agundi

3. Jihar Ribas

Rikicin jihar Ribas ya samo asali ne saboda kin amincewa da juya arzikin jihar kamar waina a tanda.

Wannan shi ne zargin da bangaren Gwamna mai ci, Siminalayi Fubara ke yiwa Ministan Abuja.

Abubuwan da su ka girgiza siyasar Ribas

1. Kokarin tsige gwamna da 'yan majaisa masu goyon bayan wike su ka yi

2. Kara wa'adin shugabannin kananan hukumomi da watanni shida da yan majalisa su ka yi, duk da wa'adinsu ya kare

3. Hukuncin da alkali Dakatima Kio ya zartar na soke kara wa'adin shugabannin kananan hukumomi

4. Tsige shugaban majalisar sarkunan Ribas, Chidi Awuse mai goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom

Ribas: 'Tinubu ya yi kokarin sasanci," Mai sharhi

Farfesa Habu Fagge masanin siyasa ne a nan Kano, ya bayyana cewa babu yadda za a yi gwamna mai ci ya bari tsohon gwamna ya rika juya akalar jiharsa.

Kara karanta wannan

Nakiya ta Tarwatsa mai Zanga Zanga Yayin da Rikicin Ribas ya Sauya Salo

Farfesa Fagge na ganin duk da yunkurin gwamnatin tarayya na shiga lamarin, kokari ne ya gyara alaka ba goyon bayan Wike ba.

Sarki Bayero ya kafa tuta a Kano

A wani labarin kun ji cewa an nada fitar sarauta a fadar Nassarawa da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ke zaune.

Wannan na zuwa duk da umarnin da gwamnatin Kano, karkashin Abba Kabir Yusuf ta ba shi na ya bar fadar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel