'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro, Sun Sace Mutum 20 a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'an Tsaro, Sun Sace Mutum 20 a Kaduna

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan wani sansanin ƴan banga a yankin Shuwaka da ke yammacin dajin Kamuku a jihar Kaduna
  • Miyagun ƴan bindigan sun hallaka ƴan banga uku a yayin harin sannan suka yi awon gaba da wasu mutane 20
  • Ɗan majalisar jihar Kaduna mai wakiltar mazaɓar Kakangi, ya tabbatar da aukuwar harin da ya bayyana a matsayin abin damuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kai hari a sansanin ƴan banga a yankin Shuwaka a yammacin dajin Kamuku da ke ƙarƙashin gundumar Kakangi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Harin wanda ya auku a yammacin ranar Talata, ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan banga uku tare da yin garkuwa da wasu mutanen ƙauyen sama da 20.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin farmaki kan bayin Allah, sun kashe jami'an tsaro

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun hallaka 'yan banga a Kaduna Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Lamarin dai na zuwa ne ƙasa da sa'o'i 48 da ƴan bindiga suka kashe ƴan banga huɗu da ɗan sanda a ranar Lahadi da yamma, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kashe ƴan banga

Wata majiya mai tushe, wacce ɗan uwanta na cikin waɗanda aka sace a harin na baya-bayan nan, ta bayyana cewa, ƴan bindigar sun farmaki sansanin ne saboda muhimmancin da yake da shi.

"An kashe ƴan banga uku da yammacin ranar Talata lokacin da ƴan bindiga suka kai hari a sansaninsu da ke yankin Shuwaka a yammacin dajin Kamuku da ke ƙarƙashin gundumar Kakangi."
"An kuma sace sama da mutane 20 daga gonakinsu a Kurgin Gabas a yankin Sabon Layi."

- Wata majiya

'Dan majalisa ya tabbatar da harin 'yan bindiga

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kakangi a majalisar dokokin jihar Kaduna, Yahaya Musa Dan Salio ya tabbatar da faruwar lamarin

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fadi lokacin da za a kawo karshen matsalar rashin tsaro a Arewa

Honarabul Yahaya Musa Dan Salio ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa.

Hakazalika, Ishaq Kasai, tsohon shugaban ƙungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari (BEPU), ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai, ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba, ASP Mansir Hassan.

Ƴan bindiga sun sace ɗan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wani jami’in ƴan sanda da kuma direban da ke aiki tare da wani basarake mai daraja a jihar Rivers.

Ƴan bindigan sun yi garkuwa da mutanen ne a ranar Asabar a gidan mai martaba, Cif Cornwell Ihunwo da ke kusa da tsibirin Eagle Island.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel