Yobe: Wata Matar Aure Ta Soka Wa Mijinta Wuka Har Lahira, Ta Yi Bayanin Abin da Ya Faru

Yobe: Wata Matar Aure Ta Soka Wa Mijinta Wuka Har Lahira, Ta Yi Bayanin Abin da Ya Faru

  • Ƴan sanda sun kama wata matar aure Zainab Isa bisa zargin daɓawa mijinta wuta har lahira a Abbari da ke cikin Damaturu a jihar Yobe
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Dungus Abdulkareem ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da saɓani ya shiga tsakanin ma'auratan
  • A kalamata, Zainab ta ce ba da gangan ta kashe sahibinta ba, akasi aka samu a kokarin kare kanta da wuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Wata matar aure ‘yar shekara 22 ta daba wa mijinta wuka har lahira a unguwar Abbari da ke Damaturu babban birnin jihar Yobe a Arewa maso Gabas.

Matar mai suna Zainab Isa yar kimanin shekara 22 ta hallaka mijinta Ibrahim Yahaya ɗan shekara 25 da wuƙa a lokacin da sa'insa ta haɗa su.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ƙasurgumin ɓarawo a Bauchi, ya sace N120m da kayayyaki rututu

Taswirar jihar Yobe.
Yan sanda sun kama matar da ake zargin ta kashe mijinta a Yobe
Asali: Original

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkareem ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Damaturu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun kama Zainab

Ya ce tuni ƴan sanda suna kama Zainab kuma rundunar ba ta ji daɗin abin da ya afku ba wanda ya zama ajalin matashin magidancin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, ofishin ‘yan sanda na C ya samu korafi daga wani makwabcinsu da ke unguwar Abbari a Damaturu, cewa ma’auratan sun samu rashin jituwa wanda ya rikide zuwa faɗa.

Ya ce makwabcin ma’auratan ya shaida wa ‘yan sanda cewa matar ta yi amfani da wuka ta daba wa mijin a kirji wanda hakan ya zama ajalinsa kafin ƴan sanda su kariso.

Kakakin ‘yan sandan ya ce sun miƙa Zainab zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID) domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da ita a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun mamaye fitaccen gari a Zamfara, dan majalisa ya nemi dauki

Zainab ta ce tsautsayi ne

Yayin da take amsa laifin a hannun ƴan sanda, matar ta ce ba ta yi niyyar kashe mijinta ba, sai dai ta yi amfani da wuƙa ne domin kare kanta, rahoton Channels tv.

Zainab ta ƙara da cewa babu wani farin ciki a zaman aurnsu, kullum cikin faɗa da tashin hankali suke musamman idan ta nemi abinci ko kuɗi daga majinta.

'Yan bindiga sun kashe mutanen Zamfara

A wani rahoton Yan bindiga sun kai hari masallaci a lokacin da mutane ke shirin sallar asuba a kauyen Tazame da ke ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe ladani da ƙaninsa, sun yi awon gaba da mutane da dama yau Talata da safe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262