Yayin da Ake Rade Radin Tuge Shi, Sultan Ya Tura Sako Ga Rundunar Sojoji

Yayin da Ake Rade Radin Tuge Shi, Sultan Ya Tura Sako Ga Rundunar Sojoji

  • Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya hori jami'an sojoji da su kaucewa duk wani lamari da ya shafi kabilanci
  • Sultan ya mika rokon ne yayin kaddamar da hedikwatar rundunar a jihar Bauchi a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024
  • Ya ce a yanzu ana yawan samun matsalolin kabilanci da bangaranci na addini da kuma yanki wanda da babu haka

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya shawarci rundunar sojoji kan aiki tukuru.

Sultan ya bukaci sojojin da su kaucewa kabilanci a yayin gudanar da ayyukansu inda ya ce hakan zai raba kasar.

Sultan ya tura sako ga rundunar sojojin Najeriya
Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar ya gargadi sojoji kan nuna kabilanci. Hoto: Sultan of Sokoto.
Asali: Facebook

Sultan ya koka game da karuwar bambance-bambance

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ƙasurgumin ɓarawo a Bauchi, ya sace N120m da kayayyaki rututu

Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne a yau Laraba 26 ga watan Yunin 2024 a Bauchi yayin kaddamar da hedikwatar sojoji, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a da ba a san da matsalolin kabilanci da addini a harkokin rundunar sojojin ba amma yanzu suna neman lalata rundunar.

"A yanzu kuna fama da matsalolin daga ina ka fito? wane addini kake? waye Hausa? waye Bayarbe? waye Igbo wanda a baya bamu san da haka ba."
"Ina rokonku kada ku bar irin wannan ya yi tasiri a cikinku wanda zai rarraba kawunanku har ma da kasar baki daya."

- Muhammad Sa'ad Abubakar III

Sultan ya ba 'yan Najeriya muhimmiyar shawara

Sultan ya kuma gargadi al'umma da ka da su rika kushe ayyukan sojojin da suke kokarin kawo zaman lafiya a kasar.

Ya ce Najeriya na bukatar addu'a musamman ga sojoji saboda idan babu tsaro ba za a iya bacci ba ko zuwa aiki ko wurin bauta.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

Gwamnatin Sokoto ta musanta tsige Sultan

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Sakkwato ta musanta zargin da MURIC ta yi na cewa tana shirin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Ta kuma bukaci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya rika bin diddigin gaskiya kafin ya yi tsokaci kan wasu muhimman batutuwan kasa.

Hakan ya biyo bayan zargin gwamnatin jihar Sokoto na shirin tuge Sarkin Musulmi daga kujerar sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.