"Ban San Aminu Ado Ba": Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Fadi Matsayarsa Kan Rigimar Kano

"Ban San Aminu Ado Ba": Kwamishinan ’Yan Sanda Ya Fadi Matsayarsa Kan Rigimar Kano

  • Kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Salman Garba ya magantu kan yadda zai yi aiki a jihar duk da rigimar sarauta
  • Sabon kwamishinan ya bayyana cewa ya zo Kano ne domin yin aiki ba kare muradun wasu tsiraru ba a jihar
  • Garba ya kuma yi fatali da labarin cewa yana da alaka da Aminu Ado Bayero inda ya ce a yau ya fara jin labarin shi ma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Kano, Salman Garba ya yi martani kan rigimar sarautar jihar.

Garba ya ce ya zo Kano ne domin aiki ga 'yan kasa da kuma Najeriya ba kare muradun wasu ba.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya kunyata 'yan siyasa a zaman makokin tsohon gwamna

Kwamishinan ƴan sanda a Kano ya magantu kan alaƙarsa da Aminu Ado
Kwamishinan ƴan sanda a Kano ya musanta alaka da Aminu Ado Bayero. Hoto: @KanoPoliceNG.
Asali: Twitter

Kano: Ƴan sanda ya magantu kan sarauta

Sabon kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da ya ke amsa tambayoyi kan yadda zai dakile rigamar sarautar jihar a cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahorannin sun yi nuni da cewa Garba yana da alaka da Aminu Ado Bayero yayin da ya fito daga jihar Kwara inda mahaifyar tsohon sarkin ta fito.

Sai dai kwamishinan yayin hirar ya ce shi ma a yanzu ya fara jin wannan labari da ake yadawa, Leadership ta tattaro.

Ya bayyana cewa ya zo Kano ne domin yin aiki ba tare da nuna wariya na addini ko wani kabilanci ba.

Salman ya musanta alaka da Aminu Ado

"Farko dai ni dan Najeriya ne kuma na zo ne domin bautawa 'yan kasar, labarin Bayero yana da alaka da ni yanzu na fara ji nima.

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

"Ni dai na zo Kano ne domin bautar jama'a kuma zan yi duka mai yiwuwa domin tabbatar da dakile matsalolin jihar."

- Salman Garba

An nada sabon Kwamishinan ƴan sandan Kano

Kun ji cewa kwamishinan ƴan sanda a Kano, Salman Garba ya karbi ragamar rundunar ƴan sandan ne daga Usaini Gumel.

Kamar yadda muka ruwaito, CP Salman Garba ya lashi takobin yin aiki tuƙuru domin wanzar da zaman lafiya a Kano da kuma kare rayuka da dukiyoyin al'ummar.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya zayyana wasu muhimman abubuwa game da rayuwar sabon kwamishinan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel