An Gano Yadda Fadar Shugaban Kasa ta Kashe N244m a Sayen Tayoyin Mota a Kwana 1

An Gano Yadda Fadar Shugaban Kasa ta Kashe N244m a Sayen Tayoyin Mota a Kwana 1

  • Ana tsaka mai wuya da matsin rayuwa a Najeriya, sai aka jiyo fadar shugaban kasa ta kashe miliyoyin Naira wajen sayen tayar motoci
  • Wani bincike ya gano cewa an sayi tayoyin mota masu sulke da wadansu tayoyin da ba a san adadinsu ba kan makudan kudi N244,654,350
  • Rahotanni na nuna cewa an sayo motocin ne a makon da aka yi bikin cikar shugaba Bola Ahmed Tinubu shekara guda a kan mulkin Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Yayin da 'yan Najeriya ke ta wayyo-wayyo saboda tsananin rashi da hauhawar farashi, an gano fadar shugaban kasa ta sayi tayoyin mota na miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta dauki mataki bayan Tinubu ya yi biris da maganar ƙarin albashi

An gano cewa fadar shugaban kasa ta kashe N244,654,350 cikin kwana daya domin sayo tayoyin mota da ba a san adadinsu ba.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Fadar shugaban kasa ta sayu tayoyin mota na N244m a kwana guda Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Binciken Daily Trust ya gano cewa fadar shugaban kasa ta fitar da kudin da aka yi odar tayoyin Westlake na motoci masu sulke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sayi tayoyin motar ne a satin da aka yi bikin cikar shugaba Bola Ahmed Tinubu shekara daya a kan mulki.

Yadda aka sayi motocin

Nairaland ta wallafa cewa takardun da aka tattaro daga shafin da ke tattara bayanai kan kashe kudin da gwamnati, govspend ta gano yadda aka sayi motocin.

An biya kudin sayen tayoyi da ba a bayyana adadinsu ba kan N200,583,390, da tayoyin motoci masu sulke guda biyar ga kamfann Obi-Wealth Enterprises Nigeria Limited kan kudi N38,070,000.

Kara karanta wannan

Aure mai dadi: Mawaki Davido gwangwaje amaryarsa da kyautar motar alfarma

An bayar da N6,000,960 ga kamafanin Hommy & Fay Investments Limited shi ma domin sayo wasu tayoyin.

Fadar Aso Rock: An sanya jirage a kasuwa

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanya jiragen fadar shugaban kasa guda uku a kasuwa saboda rage kudin da akae kashewa a kansu.

A yanzu haka, fadar shugaban kasa na da jirage guda shida, da masu saukar ungulu guda hudu da shugaban kasa ke ajiye a fadar gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel