Annobar Kwalara Ta Yaɗu a Jihar Kano? Gaskiya Ta Fito

Annobar Kwalara Ta Yaɗu a Jihar Kano? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana halin da ke ciki bayan an saka jihar a cikin jerin garuruwan da annobar kwalara ta bulla a Najeriya
  • Jami'in yada labaran ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Kano, Ibrahim Abdullahi ya bayyanawa manema labarai halin da ake ciki a jihar
  • Hukumar kula da yaɗuwar cututtuka ta kasa (NCDC) ce ta yi ikirarin cewa jihar Kano na cikin garuruwan da annobar kwalara ta bulla

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Ma'aikatar lafiya a Kano ta yi bayani kan halin da ake ciki a jihar bayan annobar kwalara ta bulla a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan hukuma mai kula da yaɗuwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta ayyana Kano cikin jihohin da suke fama da kwalara.

Kara karanta wannan

"Ban san Aminu Ado ba": Kwamishinan 'yan sanda ya fadi matsayarsa kan rigimar Kano

Jihar Kano
Gwamnati ta ce babu kwalara a Kano. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami'in yada labaran ma'aikatar lafiya ta Kano, Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin jiha ta ce babu kwalara a Kano

Ibrahim Abdullahi ya tabbatarwa manema labarai cewa annobar kwalara ba ta bulla jihar Kano ba, rahoton Daily Post.

Jami'in lafiyar ya ce a binciken da suka yi a yau Laraba ya nuna cewa babu ko mutum daya da ya kamu da kwalara a jihar Kano.

Kwalara: 'Mu ma haka muka ji labari'

Yayin da aka tambaye jami'in lafiyar kan bayanan da hukumar NCDC ta fitar a kan bullar kwalara a Kano, sai ya ce:

'Muma haka muka ga rahoton na yawo a kafafen sadarwa amma mu a Kano bamu da mai cutar kwalara ko daya'

-Ibrahim Abdullahi, kakakin ma'aikatar lafiyar Kano

Maganar da NCDC ta yi kan Kano

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Hukumar NCDC ta bayyana cewa an samu mutane 1,141 da suka kamu da cutar kwalara daga watan Janairu zuwa 11 ga Yunin 2024.

NCDC ta kuma yi ikirarin cewa akwai mutane 13 da suka kamu da cutar a jihar Kano duk da cewa hukumar lafiya a jihar ta musanta ikirarin.

Kwalara ta bulla a jihar Legas

A wani rahoton, kun ji cewa an samu barkewar annobar kwalara a wasu kananan hukumomin jihar Legas da ke kudu maso yamman Najeriya.

Gwamnatin jihar Legas ta ce annobar ta harbi mutane da dama kuma ta jawo asarar rayuka a wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng