Atiku Ya Koka Kan Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Manyan Arewa, 'Dan Siyasar Ya Fadi Mafita

Atiku Ya Koka Kan Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Manyan Arewa, 'Dan Siyasar Ya Fadi Mafita

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana mafita kan yadda yan bindiga suka fara kashe manya a Arewa
  • Atiku Abubakar ya yi martani ne bayan da yan bindiga sun kashe mataimakin shugaban jami'ar UDUS da wani Birgediya Janar
  • Har ila yau, Atiku ya mika sakon ta'aziyya a madadin iyalansa ga daukacin iyalan manyan mutanen da yan bindigar suka hallaka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Biyo bayan yawaitar kisan yan bindiga da aka samu a kwanan nan a Arewacin Najeriya, Atiku Abubakar ya yi martani.

Atiku Abubakar ya yi martani mai zafi bayan kisan mataimakin shugaban jami'ar Usmanu Danfodiyo, Farfesa Yusuf Saidu da wani babban soja.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

Atiuku Abubakar
Atiku ya fadi mafita kan rashin tsaro. Hoto: Usmanu Danfodiyo University, Sokoto|Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Legit ta gano haka a cikin wani sako da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya yi Allah wadai da hare-hare

A cikin sakon da ya wallafa, Atiku Abubakar ya ce abin Allah-wadai ne yadda yan bindiga suka kashe Farfesa Yusuf Saidu da Birgediya Janar Harold Udokwere (Mai ritaya).

Atiku ya ce wannan kawai ya kai ya sa Najeriya ta dauki matakin da ya kamata domin shawo kan matsalolin tsaro.

Atiku: "Hanyar magance matsalolin tsaro"

Atiku Abubakar ya bayyana cewa hanya daya da za a bi wajen magance matsalolin tsaron Najeriya shi ne sake garambawul ga tsarin tsaron kasar.

Sai kuma a samu canjin gwamnati da za ta samar da abin da ake bukata wajen tabbatar da tsaron yan kasa.

Atiku Abubakar ya tura sakon ta'aziyya

Kara karanta wannan

Nakiya ta Tarwatsa mai Zanga Zanga Yayin da Rikicin Ribas ya Sauya Salo

Har ila yau, Atiku Abubakar ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan Farfesa Yusuf Saidu da Birgediya Janar Harold Udokwere.

'Dan takaran shugaban kasar ya ce yana taya rundunar sojin Najeriya da jami'ar Usmanu Danfodiyo jaje bisa rashin da suka yi.

'Dan majalisa ya koka kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da aka kammala taron yadda za a shawo kan matsalolin tsaro a jihohin Arewa maso yamma a Katsina, dan majalisa a Zamfara ya koka.

'Dan majalisa, Rilwanu Marafa Na Gambo ya ce yan ta'adda na kashe jama'arsa babu dare babu rana, kuma su yi tafiyarsu ba tare da an kama su ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng