Zargin Satar N432bn: El Rufai Ya Ɗauki Matakin Shari’a Kan Majalisar Dokokin Kaduna
- Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya dauki matakin shari'a kan majalisar dokokin jihar
- Malam El-Rufai ya garzaya kotu ne a ranar Laraba inda ya nemi a rusa rahoton majalisar da ya ce gwamnatinsa ta karkatar da N432bn
- Tsohon gwamnan, wanda ya shigar da karar a kan tauye hakki ya ce majalisar Kaduna ba ta bashi damar kare kansa daga zarge zargen ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu kan zarginsa da ta yi da karkatar da N432bn a shekaru takwas na mulkinsa da kuma barin dimbin bashi.
A ranar Larabar nan ne El-Rufai ya shigar da kara kan take 'yanci a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda ya ke ƙarar majalisar dokoki.
El-Rufai ya maka majalisar Kaduna a kotu
Rahoton Channels TV ya nuna lauyan tsohon gwamnan, Abdulhakeem Mustapha SAN ne ta shigar da karar idan yake ƙalubalantar matakin majalisar na tuhumar El-Rufai da laifin 'zamba.'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin takardar karar El-Rufai ya nemi kotun da ta rusa rahoton binciken majalisar dokokin sakamakon ba a ba shi damar kare kansa kan zarge zargen da ake yi masa ba.
Baya ga majalisar dokokin Kaduna, El-Rufai ya haɗa da Antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar a cikin wadanda yake kara.
El-Rufai: Dalilin yin karar majalisar Kaduna
Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Muyiwa Adekeye, ya wallafa a shafinsa na X cewa:
"Malam Nasir El-Rufai ya dura babbar kotun tarayya da ke Kaduna domin rattaba hannu a karar da ya shigar kan majalisar dokokin jihar Kaduna a gaban kotun.
"El-Rufai ya je kotun ne a matsayinsa na ɗan Najeriya wanda ya ke da 'yanci a bashi damar kare kansa kafin wani kwamiti ko hukuma ta yanke hukunci kan hakkinsa.
"Bisa ga sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, El-Rufai na neman kotun ta rusa rahoton binciken basussuka, hada-hadar kudi da sauransu da majalisar ta zartar."
Majalisar ta yi kwamitin binciken El-Rufai
Tun a tsakiyar watan Afrilu ne muka ruwaito cewa majalisar dokokin jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda Nasir El-Rufai ya tafiyar da mulkin jihar.
Majalisar na zargin tsohon gwamnan ya karkatar da wasu kudi kuma gwamnatinsa ta ci tarin bashi ba tare da an aiwatar da wani aikin a-zo-a gani ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng