Ana Murna da Dalar Amurka Ta Ƙara Karyewa a Kasuwar Canji a Najeriya
- Farashin musayar Dalar kasar Amurka ya sauka a kasuwar ƴan canji ranar Talata idan aka kwatanta da farashin ranar Litinin dinnan
- Rahoto ya nuna cewa Naira ta ƙara daraja zuwa N1,500 daga N1,505 kan kowace Dala a kasuwar ƴan canji, amma ta faɗi a kasuwar gwamnati
- Naira ta faɗi zuwa N1,500.79/$1 a kasuwar hada-hada ta gwamnati daga N1,490.2/1$, ma'ana kuɗin Najeriya sun ragu da N10.59
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Darajar Naira ta tashi a kasuwar hada-hadar musayar kuɗi ta bayan fage ranar Talata, 25 ga watan Yuni, 2024.
Dalar Amurka ta karye zuwa N1,500 daga N1,505 da aka yi musayar kuɗin a ranar Litinin da ta gabata a kasuwar ƴan canji.
Naira ta faɗi a farashin gwamnati
Sai dai kuma darajar Naira ta ragu zuwa N1,500.79 kan kowace Dala a kasuwar canji ta Najeriya mai cin gashin kanta, NAFEM, Jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoto daga hukumar cinikayyar kuɗin waje ta kasa (FMDQ) ya nuna cewa farashin canji a NAFEM ya tashi zuwa N1,500.79/1$ daga N1,490.2/$ na ranar Litinin.
Wannan ya nuna cewa ƙimar Naira ta ragu da N10.59 a kasuwar hada-hadar kuɗi ta gwammati.
Karancin cinikin Dala a kasuwa
Adadin Dalar da aka yi ciniki a kasuwa ya ragu da kashi 10% zuwa $136.72m daga Dalar Amurka miliyan 152 da aka yi cinikayyarta a ranar Litinin da ta shige.
Sakamakon haka, tazarar da ke tsakanin kasuwar ƴan canji da farashin NAFEM ya ragu zuwa kobo 79 kan kowace Dala daga N14.8 kan kowace dala a ranar Litinin.
Ƙimar kuɗin Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen sauka da tashin farashin kayayyakin amfani na yau da kullum, wanda ƴan Najeriya ke ci gaba da kokawa kansu.
Babban banki na CBN na ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da darajar Naira tun bayan mummunar faɗuwar da ta yi, wanda ta kai kusan N2,000/1$.
CBN zai sabunta lasisin ƴan canji
A wani rahoton kuma yayin da darajar Naira ke ƙaruwa a kasuwa, babban bankin ƙasa CBN ya yi wasu sababbin sauye-sauye domin inganta ayyukan ƴan canji.
CBN ya umarci halastattun ƴan canaji su sabunta lasisin aiki kuma ya cire masu dokar ajiye wasu adadin kudi kafin a ba su lasisi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng