Emefiele: Bayan Kwace Kadarorin N12bn, Tsohon Gwamnan CBN Ya Nemi Alfarma a Kotu

Emefiele: Bayan Kwace Kadarorin N12bn, Tsohon Gwamnan CBN Ya Nemi Alfarma a Kotu

  • Godwin Emefiele ya buƙaci babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba shi izinin zuwa ganin likita a ƙasar waje
  • Tsohon gwamnan CBN ya shigar da wannan buƙata ne ta hannun lauyansa, Mathew Burkaa kuma har yanzu EFCC ba ta ce komai ba
  • Emefiele na ci gaba da fuskantar shari'a kan tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa bayan shugaban ƙasa ya sauke shi daga mukaminsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya buƙaci babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba shi izinin fita ƙasar waje.

Mista Emefiele ya nemi izinin tafiya waje domin a duba lafiyarsa a gaban kotun da yake fuskar shari'a kan tuhume-tuhumen satar kuɗin baitul-mali.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauki mataki kan sabon mafi ƙarancin albashi a taron majalisar zartarwa

Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Godwin Emefiele ya nemi izinin fita ƙasar wajen domin duba lafiyarsa Hoto: Mr.Godwin Emefiele
Asali: Twitter

Lauyan tsohon gwamnan CBN, Mathew Burkaa ne ya tunatar da alƙalin kotun game da wannan buƙata a zaman ranar Talata, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Emefiele ke son tafiya ƙasar waje?

Sai dai lauyan bai yi cikakken bayani kan rashin lafiyar da ke damun Emefiele ba da har ta kai ga yake neman izinin zuwa ganin likita.

Idan ba ku manta ba Alkalin kotun, Hamza Mu’azu, ya bayar da umarnin a kwace fasfon Mista Emefiele a wani bangare na sharudɗan belinsa.

Don haka ne tsohon gwamnan ya nemi a ba shi fasfonsa domin ya tafi ganin likitansa a ƙasar waje.

Mai shari'a Mu'azu ya sanya ranar 8 ga watan Yuli, 2024 domin sauraron buƙatar wanda ake ƙara da kuma yiwuwar yanke hukunci, rahoton Ripples Nigeria.

Har kawo yanzu, hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ba ta ce komai ba game da buƙatar Emefiele.

Kara karanta wannan

NLC: Ƴan kwadago sun roki Tinubu, sun faɗi mafi ƙarancin albashin da suke buƙata

EFCC na tuhumar Emefiele da laifufuka 20

A shari’ar, EFCC na tuhumar Emefiele da laifuka 20 da suka hada da buɗe ƙofar cin hanci da rashawa, hada baki, zagon kasa, ƙarya, da kuma karbar kusan $6.23m ba bisa ka'ida ba.

Tun da Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga kujerar gwamnan CBN a watan Yuni, Emefiele ke fuskantar shari'a kan tuhumar almundahana a Abuja da Legas.

Hukumar EFCC ta bankaɗo rabon kwangila a CBN

A wani rahoton kun ji cewa hukumar EFCC ta shaidawa kotu zargin da ta ke na yadda tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele ya yi watandar kwangila.

Shaidan EFCC na bakwai ya ce tsohon shugaban babban bankin kasa, Mista Emefiele ya raba kwangiloli ga mai dakinsa da dan uwanta a zamaninsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262