Mafi Ƙarancin Albashi: Jigon PDP Ya Fadi Abin da Jihohi Za Su Iya Biyan Ma’aikata
- Wani jigon jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju ya ce gwamnonin jihohi na da karfin ikon biyan N100,000 matsayin mafi ƙarancin albashi
- A tattaunawar Rilwan da Legit.ng, ya ce a kyale gwamnoni su biya ma'aikata gwargwadon abin da suke samu daga tarayya da kuma haraji
- Jigon jam'iyyar adawar ya koka kan yadda wasu gwamnoni ke gaza alkinta albarkatun kasa da ke jihohinsu wajen samar da kudaden shiga
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Wani jigon jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju ya ce gwamnonin Najeriya na da karfin ikon biyan N100,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata.
A zantawarsa da Legit.ng, Mista Rilwan ya nemi a kyale gwamnoni su biya mafi ƙarancin albashin gwargwadon abin da suke samu daga tarayya da kuma haraji.
Jigon PDP magantu kan mafi ƙarancin albashi
Ya jaddada bukatar kungiyoyin kwadago su nemi hanyar sasantawa da gwamnoni kan mafi ƙarancin albashi bayan jihohi sun ki amincewa da tayin N62,000.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon jam'iyyar adawar ya ce:
"Matsalolin kasarmu na da yawa. Muna da shugabanni masu son kansu, wadanda ba sa da hangen nesa. Ina ganin a bar kowanne gwamna ya biya abin da zai iya.
"Ya kamata su ma jama'a su dawo zabar wanda ya cancanta ba wai sanayya ko kudi ba. Kowacce jihar Najeriya na da karfin ikon biyan N100,000 matsayin mafi ƙarancin albashi."
Jihohi masu iya biyan albashin N100,000
Jigon jam'iyyar na PDP ya lissafa jihohin Najeriya da ke da karfin tattalin arzikin biyan ma'aikata N100,000 matsayin mafi ƙarancin albashi.
A cewarsa:
"Jihohi kamar Bayelsa, Legas, Rivers, Akwa Ibom da Delta na da karfin ikon biyan mafi ƙarancin albashi mai tsoka saboda kudin da suke samu daga tarayya na da yawa.
"Kamar Bayelsa, tana da kasa da mutane miliyan hudu, amma tana samun sama da kaso 85% na abin da jihohi ke samu, ya kamata ta rika biyan ma'aikata albashi mai tsoka.
"Ba na tunanin ko nawa aka biya ma'aikata ya zama ya yi yawa, la'akari da tsadar kayayyaki ya haura zuwa kashi 33.95%. Ya kamata shugabanni su nuna sun damu da ma'aikatan."
Jihohi masu biyan ma'aikata albashin N30,000+
A wani labarin, mun ruwaito cewa akwai jihohin Najeriya da tuni suka koma biyan ma'aikatansu sama da N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Biyo bayan matsin tattalin arziki da tsadar kayan masarufi, bukatar a yi karin albashi ga ma'aikata ya tsananta a fadin Najeriya, yayin da 'yan kwadago ke kai ruwa rana da gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng