Bola Tinubu Ya Ɗauki Mataki Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi a Taron Majalisar Zartaswa
- Majalisar zartaswa ta FEC a karkashin Bola Ahmed Tinubu ta jingine rahoton kwamitin sabon mafi ƙarancin albashi a taron yau Talata
- Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ya ce majalisar ta yi haka ne domin bai wa Tinubu lokacin ji daga kowane ɓangare
- Ya ce kwamitin da aka kafa kan sabon albashin ya miƙa rahotonsa amma ba zai yiwu FEC ta ɗauki mataki ba, duba da lamarin ya shafi ɓangarori da dama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta jingine kundin da aka gabatar kan sabon mafi karancin albashi a taron yau Talata a Aso Villa.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma na ƙasa, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar a fadar gwamnatin Najeriya.
Batun mafi karancin albashi a zaman FEC
Mohammed Idris ya shaidawa masu ɗauko rahoton gidan gwamnati cewa batutuwa 39 aka gabatar a taron yau kuma majalisar ta duba su duka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangane da batun mafi ƙarancin albashi, ministan ya tabbatar da cewa kwamitin da aka kafa ya miƙa rahoton aikin da ya yi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kwamitin mafi karancin albashin da aka kafa ya ƙunshi wakilan kananan hukumomi, jihohi, kungiyoyin kwadago NLC da TUC da kuma gwamnatin tarayya.
FEC ta kara ba Bola Tinubu lokaci
Miinistan ya ce majalisar ba za ta iya yanke hukunci a kan batun ba saboda ya shafi kananan hukumomi, jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da ƴan kwadago.
Bisa haka ne majalisar ta ga ya dace ta jingine batun domin bai wa shugaban ƙasa damar tattaunawa da jin ta bakin kowane ɓangare kafin ɗaukar matsaya.
A cewarsa, Tinubu zai sake nazari kuma ya nemi shawarwari kafin ya miƙa kudirin sabon albashin ga majalisar tarayya, Channels tv ta ruwaito.
NLC ta nemi Tinubu ya ɗauki N250,000
A wani rahoton na daban kuma, ƙungiyar kwadago ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya nuna ƙaunar da yake yiwa ma'aikata ta hanyar amincewa da N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
NLC ta bayyana cewa hakan ne kaɗai zai sa ma'aikata su samu sauƙi duba da kunci da wahalhalun rayuwar da aka shiga a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng