Babban Jami'in Hukumar Kwastam Ya Mutu Ana Tsakiyar Zaman Kwamitin Majalisa

Babban Jami'in Hukumar Kwastam Ya Mutu Ana Tsakiyar Zaman Kwamitin Majalisa

  • An tafka babban rashi bayan mutuwar wani babban jami'an hukumar Kwastam a cikin Majalisar Tarayya a Abuja
  • Marigayin ya rasu ne bayan ya fadi kasa yayin da mambobin kwamitin Majalisar kan binciken kudi ke yi masa tambayoyi
  • An kwashi DCG Essien Etop Andrew zuwa asibiti bayan ya yi tari ya fadi, a asibiti aka tabbatar da mutuwarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Wani babban jami'in hukumar kwastam ya riga mu gidan gaskiya a Majalisar Tarayya da ke Abuja.

Marigayin mai suna Essien Etop Andrew ya rasu ne yayin da yake amsa tambayoyi daga mambobin Majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 3 da ya dace a sani a kan jami'in kwastam da ya mutu a majalisa

Babban jami'in Kwastam ya mutu ana tsaka da masa tambayoyi a Majalisa
Jami'in Kwastam, Essien Andrew ya mutu yayin amsa tambayoyi a Majalisar Tarayya. Hoto: House of Representatives.
Asali: Facebook

Jami'in Kwastam ya mutu a cikin Majalisa

Kafin rasuwarsa, Andrew mataimakin kwanturola Janar a bangaren gudanar kudi na hukumar da ke Abuja a cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kadan bayan faduwarsa, an kwashi Andrew zuwa asibiti inda aka tabbatar da rasu nan take.

Kafin faduwarsa, an tabbatar da cewa sai da Andrew ya yi tari kafin ya kife kasa cikin Majalisar, The Nation ta tattaro.

Majalisar ta yi martani kan mutuwar jami'in

Mai magana da yawun Majalisar, Akintunde Rotimi ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata 25 ga watan Yunin 2024.

"Cikin jimami da nadama muke sanar da mutuwar daya daga cikin manyan jami'an hukumar Kwastam wanda ya rasu a yau yayin amsa tambayoyi daga kwamitin Majalisar."
"Yayin tambayoyin a yau Talata da misalin karfe 1:00 na rana, jami'in ya gamu da tsautsayin matsalar lafiya, duk da kokarin ceto rayuwarsa da aka yi amma abin takaici ya rasu."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ɗauki mataki kan sabon mafi ƙarancin albashi a taron majalisar zartarwa

"Saboda mutuntawa ga iyalansa za mu boye sunansa a halin yanzu zuwa wani lokaci."

- Akintunde Rotimi

Shugaban Majalisar, Abbas Tajudden ya nuna alhini tare da tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin.

Majalisa ta nemi sayawa Tinubu jirgin sama

Kun ji cewa Majalisar Wakilai ta nemi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sayen sabon jirgin sama wanda shugaban kasa da mataimakinsa za su rika hawa.

Kwamitin Majalisar kan harkokin tsaro ya ba da umarnin yana mai nuna cewa Bola Tinubu da Kashim Shettima na bukatar sabon jirgin sama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.