"Mutanen Kano Ba Su Goyon Bayan Rushe Sarakuna da Maido Sanusi II," Dan'agundi

"Mutanen Kano Ba Su Goyon Bayan Rushe Sarakuna da Maido Sanusi II," Dan'agundi

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sahihin Sarkin Kano, Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Dan'agundi ya bayyana matsayar mutanen jihar kan rikicin
  • Sarkin dawaki babba da ya shigar da gwamnatin Kano kotu kan rushe masarautun ya bayyana cewa da yawa daga al'ummar ba su amince da matakin ba
  • Dan'agundi ya kuma ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta bi hanyar da ta dace wajen tumbuke rawanin Muhammadu Sanusi II ba kamar yadda gwamnatin NNPP ta yi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Dan'agundi ya bayyana damuwa kan yadda dambarwar masarautar Kano ta ki ci, ta ki cinyewa.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Babban lauya ya bayyana sahihin Sarkin Kano

Sarkin Dawaki Babba ya shigar da kara gaban babbar kotun tarayya ya na kalubalantar matakin da gwamnatin Kano ta dauka na rushe sarakunan da tsohuwar gwamnati ta kafa.

Masarauta
Sarkin dawaki babba ya ce mutanen Kano ba su goyon bayan rushe masarautu Hoto: @HrhBayero/ Muhammad Sanusi II
Asali: Twitter

Arise Television ta wallafa cewa Aminu Babba Dan'agundi ya ce kusan 80% na jama'ar Kano ba su goyon bayan matakin da majalisar dokokin jihar ta dauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dalilan da ya sa na yi kara," Dan'agundi

Sarkin Dawaki Babba, Aminu babba dan'agundi ya bayyana dalilansa na tuhumar rushe sarakunan Kano da gwamnati Abba Kabir Yusuf ta yi.

Daily News24 ta wallafa cewa Dan'agundi ya ce majalisa ba ta bi tsari da dokokin da ya kamata ba kafin ta zartar da kudurin zuwa duka.

Tsige Muhammadu Sanusi II a Kano

Ya kare gwamnatin Abdullahi Ganduje na tsige sarki Muhammadu Sanusi II, inda ya ce sai da aka bi doka ta hanyar aika masa da takardar tuhuma kan zargin da ake masa.

Kara karanta wannan

'Aminu Ado Bayero a makabarta yake zaune ba fadar Sarki ba' Inji Gwamnatin Abba

Sarkin dawaki babba ya kuma kalubalanci yadda sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi ke caccakar masu rike da mukaman siyasa a bainar jama'a, lamarin da ya ce bai dace ba.

Kotu ta yi hukunci kan rikicin masarauta

A baya mun kawo labarin cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci kan rushe masarautun Kano da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi.

Mai shari'a Abdullahi Muhammad Limana hukuncin da ya zartar ya jingine dokar da ta maido Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan karagarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.