NELFund: Gwamnati Ta Rufe Ba da Rancen Kuɗin Karatu Ga Ɗaliban Jami'o'in Jihohi

NELFund: Gwamnati Ta Rufe Ba da Rancen Kuɗin Karatu Ga Ɗaliban Jami'o'in Jihohi

  • Hukumar kula da asusun NELFund ta dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin karatu
  • A cewar wata sanarwa da NELFund ta fitar a ranar Talata, dakatarwar za ta ba makarantun damar dora bayanan dalibansu
  • Hukumar ta koka kan yadda ƙalilan daga cikin manyan makarantun suka dora bayanan dalibansu domin tantance lamunin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da asusun ba ɗalibai rancen kudin karatu NELFund ta dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin.

Hukumar ta sanar da dakatarwar wadda za ta dauki tsawon kwanaki 14 biyo bayan karancin daliban manyan makarantun jihohi da ke neman bashin.

Kara karanta wannan

Ana jita jitar tsige Sarkin Musulmi, Atiku ya ba da shawara 1 ta kare martabar sarakuna

NELFund ta yi magana kan daliban manyan makarantun jihohi
NELFund ta dakatar da ba daliban manyan makarantu jihohi rancen kudi. Hoto: Scholarship Region, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A ranar Talata ne The Punch ta ruwaito hukumar NELFund ta ce dakatarwar ya zama wajibi saboda gazawar manyan makarantun na dora bayanan dalibansu a shafinta na intanet.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NELFund ta dakatar da ba dalibai rance

Hukumar wadda ta fitar da sanarwar a Abuja, ta ce har kawo yanzu kalilan ne daga jami'o'in jihohin kasar nan suka dora bayanin dalibansu domin tantancewa.

Sanarwar ta ce:

"Mun dakatar da ba daliban manyan makarantun jihohi damar neman rancen kudin saboda ƙalilan daga makarantun ne suka dora bayanan dalibansu a shafinmu.
"Jami'o'i 20 cikin 48, kwalejoji 12 cikin 54, kwalejin kimiyya 2 cikin 49 na jihohi ne kawai suka iya dora bayanan dalibansu.
"Gazawar manyan makarantun jihohi na dora bayanan dalibansu zai kawo cikas ga kokarinmu na ganin mun tantance masu neman rancen kudin."

Yaushe NELFund za ta janye dakatarwar?

Kara karanta wannan

Yadda kwankwaɗar kunun aya ya hallaka mutane 24, Gwamna ya dauki mataki mai tsauri

Sanarwar ta yi bayanin cewa dakatarwar za ta fara aiki daga ranar 25 ga watan Yunin 2024 zuwa ranar 10 ga watan Yulin 2024 in ji rahoton The Guardian.

Hukumar ta ce wannan zai ba manyan makarantun jihohi damar dora bayanan dalibansu a shafin hukumar na intanet domin tantancewa.

Hukumar NELFund ta kara jaddada muhimmancin ba da lamunin ga dalibai wanda ta ce zai taimaka wajen ganin dalibai sun yi karatu mai zurfi.

Abba zai gwangwaje manoma da taki

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince a sayo takin Naira biliyan 5 domin tallafawa manoman jihar.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, Abba ya ce tallafin zai bunkasa noma da kuma tabbatar da wadatuwar abinci a fadin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.