Karin Albashi: Kalaman Tinubu Ya Fusata NLC, 'Yan Kwadago Sun Yi Martani Mai Zafi

Karin Albashi: Kalaman Tinubu Ya Fusata NLC, 'Yan Kwadago Sun Yi Martani Mai Zafi

  • Kungiyar kwadago ta sake kira ga shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan karin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Najeriya
  • Wani dan kwamitin tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan karin albashi, Adewale Adeyanju ne ya jaddada abin da suke so a biya
  • An dade ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago kan karin albashi amma an kasa samun matsaya har yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar kwadago ta kara fitar da bayani kan akallan abin da take so gwamnatin Bola Tinubu ta biya ma'aikatan Najeriya.

Hakan ya biyo bayan wasu kalamai da shugaban kasa ya yi ne a kan cewa zai biya ma'aikata ne abin da zai samu lura da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

'Bashi bai amfanar talaka', an bukaci binciken yadda Najeriya ke kashe bashin da ta ci

Kungiyar Kwadago
NLC ta bukaci a biya ma'aikata N250,000. @NLCHeadquaters
Asali: Twitter

Wani dan kwamitin kungiyar kwadago da suke tattaunawa da gwamnati, Adewale Adeyanju ne ya jaddada matsayarsu ga jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Albashin da NLC ke buƙata a yanzu

'Dan kwamitin karin albashin, Adewale Adeyanju ya ce NLC ba za ta amince da karin albashi ga ma'aikatan Najeriya kasa da N250,000 ba.

Adewale Adeyanju ya ce yin hakan zai saukakawa ma'aikata tsananin rayuwa da magance tashin farashi da ake fama a Najeriya.

NLC: "Gwamnoni na kawo matsalar karin albashi"

Kwamred Adewale Adeyanju ya ce wasu daga cikin gwamnonin jihohi na kawo tsaiko kan kokarin da NLC ke yi na ganin an yiwa ma'aikata karin albashi.

Ya ce gwamnonin da suka fi kawo matsala sune wadanda suka gagara fara biyan ma'aikata N30,000 har yanzu.

Karin albashi: komai na hannun Tinubu

Sai dai duk da kalubalen da NLC ke fuskanta ta ce a yanzu haka komai na hannun shugaba Bola Tinubu domin shi zai bayyana matsaya ta karshe.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

NLC ta ce ya kamata Bola Tinubu ya nuna halin tausayi ya biya ma'aikatan abin da zai ishe su yin rayuwa a halin da ake ciki, rahoton Leadership.

An shawarci Tinubu kan karin albashi

A wani rahoton, kun ji cewa dangane da sabon mafi karancin albashi, Reno Omokri ya dage cewa Najeriya ba za ta iya biyan adadin da 'yan kwadago ke nema ba.

Omokri ya ce bai kamata gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar da mafi karancin albashin da gwamnatocin jihohi ba za su iya biya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel