"Muna Cikin Wani Hali": 'Yar Marigayi Ado Bayero Ta Nemi Taimakon Sanusi II da Abba

"Muna Cikin Wani Hali": 'Yar Marigayi Ado Bayero Ta Nemi Taimakon Sanusi II da Abba

  • Ɗiyar marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero ta bukaci taimako daga Gwamna Abba Kabir da Muhammadu Sanusi II
  • Zainab Ado Bayero ta nemi alfarma ne bayan kokarin korarta da mahaifiyarta da kuma kaninta saboda rashin biyan kudin haya
  • Wannan baiwar Allah ta kuma bukaci Gwamna Alex Otti na Abia ya taimake su inda ta ce ta tura masa sakwanni kan lamarin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Ƴar marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero ta nemi taimako daga Muhammadu Sanusi II da Gwamnan Abba Kabir.

Zainab Ado Bayero ta nemi alfarma ne yayin da ake musu barazanar kora da mahaifiyarta da kaninta daga otal a Lagos.

Kara karanta wannan

Gwamma ya faɗi gaskiya kan shirin tsige Mai aAfarma Sarkin Musulmi a Najeriya

Zainab Ado Bayero ta nemi alfarma daga Abba Kabir da Sanusi II
Diyar marigayi Ado Bayero ta bukaci taimako daga Sarkin Kano, Sanusi II da Gwamna Abba Kabir. Hoto: @Kyusufabba, @masarautarkano.
Asali: Twitter

Zainab Ado Bayero tana cikin wani hali

Ƴar marigayin ta ce ta yi kokarin rufe abin amma ya fi karfinta inda ta nemi alfarma wurin Gwamna Alex Otti na Abia, cewar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zainab ta koka inda ta ce tun bayan mutuwar mahaifinsu ba su da iko kan gidaje da kadarorinsa.

"Mun yi kokarin rokon wasu manyan mutane da ke kusa da mahaifinmu domin siya mana gida da inganta kasuwanci amma abin ya ci tura."
"Daga cikinsu akwai marigayi Maitama Sule da marigayi tsohon sarkin Zazzau da kuma marigayi Tony Momoh wanda kawun mahaifiyarmu ne amma a banza."
"A matsayina na ƴar gidan sarauta daga Kano na yi kokarin boye abin amma ya fi karfina saboda boyewan ya hana gwamnati taimakonmu ko kuma wasu makusantan mahaifinmu a Arewa."

- Zainab Bayero

Zainab ta nemi taimakon Abba, Sanusi II

Kara karanta wannan

Rusa fadar Nasarawa: Gwamnatin Abba ta ba Aminu Bayero sabon umarni a Kano

Zainab ta ce sun shafe watanni biyu a wani otal amma sun gagara biyan kudi saboda halin da suke ciki.

"Manajan bankin ya bukaci mu tashi jiya Litinin 24 ga watan Yunin 2024 da misalin 12.00 na dare inda ya kawo ƴan sanda amma muna ci gaba da rokonsu."
"Ina bukatar Alex Otti ya shiga wannan lamari, saboda na tura masa sako ta hannun J. Martin's amma har yanzu ban samu martani ba."
"Ina rokon Sanusi II wanda ya san halin da muke ciki da Gwamna Abba Kabir su kawo mana ɗauki, ina fatan zaman lafiya a Kano."

- Zainab Ado Bayero

"Aminu Ado ne Sarkin Kano" - Abba Hikima

Kun ji cewa fitaccen lauya a jihar Kano, Abba Hikima ya yi tsokaci kan dambarwar sarautar jihar Kano.

Hikima ya ce a mahangar shari'a a yanzu Aminu Ado Bayero shi ne sahihin Sarkin Kano bayan yanke hukuncin kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.