A Ƙarshe, Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Ruguza Arewa, Ya Nemo Hanyoyin Dakile Matsalolin

A Ƙarshe, Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Ruguza Arewa, Ya Nemo Hanyoyin Dakile Matsalolin

  • Shugaba Bola Tinubu ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara ƙamari musamman a Arewa maso Yamma
  • Tinubu ya danganta matsalar da rashin adalci da ake yi tun farko wanda ya farraka al'ummu a yankin da ma Arewacin kasar gaba daya
  • Shugaban ya bayyana haka ne yayin taron kwanaki biyu na gwamanonin Arewa maso Yamma kan matsalar tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana babban dalilin ƙaruwar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Tinubu ya ce rashin tsaro ya samo asali ne daga rashin adalci da ake yiwa wadanda abin ya shafa.

Tinubu ya nemo mafita kan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya
Bola Tinubu ya nuna damuwa kan ƙaruwar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Arewa: Tinubu ya fadi musabbabin matsalar tsaro

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

Shugaban ya kuma zargi gwamnatocin baya da sakaci kan matsalar wanda gwamnatinsa ta gada, Punch ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima wanda ya wakilci Tinubu shi ya bayyana haka a taron gwamnonin Arewa maso Yamma kan matsalar tsaro.

"Matsalar rashin tsaro a Arewa maso Yamma ba abu ne da aka kirkira na yanki domin cimma wani buri ba."
"Mun samar da hanyoyin dakile wannan matsalar tsaro da muka gada tun kafin fara wannan tafiya."
"Mun gano cewa kawo karshen wannan matsala dole sai an koma baya saboda rashin adalci da ya farraka al'ummu da dama a yankin."

- Kashim Shettima

Muhimmacin Arewa maso Yamma ga Najeriya

Wakiliyar hukumar UNDP a Najeriya, Elsie Gyekyeua Atafauh ta bayyana muhimmacin Arewa wurin daga darajar kasar a Nahiyar Afirka.

Atafauh ta ce idan ana son Najierya ta ci gaba da rike kambunta na giwar Afirka dole sai an ba Arewa maso Yamma kulawa na musamman.

Kara karanta wannan

Ta'addanci a Najeriya: Za a gudanar da gagarumin taro irinsa na farko a Arewa

Kashim ya magantu kan zargin tuge Sultan

Kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya magantu kan zargin cire Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar daga sarauta.

Shettima ya yi gargadi inda ya ce Sultan ba iya Sarkin Sokoto ba ne kadai yana jagorantar al'ummar Musulmai ne gaba daya a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan zargin kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC na cewa gwamnan Sokoto na kokarin tube Sultan daga sarauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel