Kwankwaso Zai Fara Gwabzawa da EFCC a Kotu Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano

Kwankwaso Zai Fara Gwabzawa da EFCC a Kotu Ana Tsaka da Rikicin Sarautar Kano

  • Rabiu Kwankwaso da wasu mutum bakwai sun shigar da ƙarar hukumar EFCC gaban babbar kotun jihar Kano kan yunƙurin take haƙƙinsu
  • Yayin da aka gabatar masa da ƙarar, mai shari'a Yusuf Ubale ya sanar da cewa kotu za ta fara sauraron ƙarar ranar 11 ga watan Yuli, 2024
  • Kotun ta hana hukumar EFCC musgunawa ko kama masu ƙara har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci a shari'ar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar kotun Kano da ke zamanta a Audu Baƙo za ta fara zaman sauraron ƙorafin da Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutum bakwai suka shigar da EFCC.

Jagoran NNPP da sauran mutanen su bakwai sun maka hukumar yaƙi da rashawa EFCC a gaban kotun ne kan abin da ya shafi tauye haƙƙinsu.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta dauki mataki a shari'ar tsige Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kotu za ta fara zaman shari'ar da Kwankwaso ya shigar da EFCC a watan Yuli Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da jam'iyyar NNPP, Dr. Ajuji Ahmed, Dipo Olayanku, Ahmed Balewa, Cif Clement Anele, Lady Folshade Aliu, Buba Galadima da Kwankwaso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ce kaɗai ake ƙara a shari'ar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kotu za ta fara sauraron ƙarar Kwankwaso

Yayin da aka gabatar da ƙarar gaban Mai shari'a Yusuf Ubale Muhammad ranar Litinin, lauyan masu kara ya shaidawa kotu cewa sun sanar da EFCC batun ƙarar.

Barista Robert Hon ya faɗawa alkalin cewa sun sanar da EFCC batun shari'ar ranar 10 ga watan Yuni, kuma bisa doka ya kamata su amsa cikin mako ɗaya.

Amma a nasa ɓangaren, Mai Shari'a Yusuf Ubale ya ce ya kamata a bai wa waɗanda ake tuhuma isasshen lokaci domin su dawo da amsa kan shari'ar.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta tanadi hukunci kan tsige ƴan majalisa 27 da suka bar PDP zuwa APC

Sakamakon haka alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 11 ga watan Yuli, 2024 domin fara zama kan gundarin shari'ar.

Kotun ta hana EFCC kamawa, tsoratarwa ko musgunawa Kwankwaso da sauran waɗanda ke ƙara har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci, rahoton Vanguard.

EFCC ta taso Kwankwaso a gaba

A wani rahoton kuma Hukumar EFCC ta fara bincike kan zargin da ake yiwa Rabiu Musa Kwankwaso da karkatar da N2.5bn.

Kuɗaɗen da ake zargin Kwankwaso da tawagarsa sun karkatar na yaƙin neman zaɓen jam'iyyar NNPP ne a lokacin zaɓen shekarar 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262