EFCC Ta Shaidawa Kotu Yadda Emefiele ya yi Tuwona Maina Wurin Bada Kwangilar CBN
- Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta shaidwa kotu zargin da ta ke na yadda tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele ya yi watandar kwangila
- Shaidan EFCC na bakwai ya shaidawa kotu cewa tsohon shugaban babban bankin kasa, Mista Emefiele ya raba kwangiloli ga mai dakinsa da dan uwanta a zamaninsa
- Sai dai da lauyan Emefiele, Mathew Burkaa SAN ya tambaye shi ko akwai shaidar wanda ya ke karewa ya samu wani kaso na kudin kwangilar, shaidan, Micheal Agboro ya ce a'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja- Hukumar EFCC ta zargi tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele da rashin gaskiya wurin bayar da kwangiloli daga cibiyar kudin kasar nan.
A zaman kotu da aka gudanar, shaidan EFCC na bakwai, Michael Agboro, ya bayyana cewa Emefiele ya bayar da kwangiloli ga kafanin matarsa, har da na dan uwanta.
Daily Trust ta wallafa cewa hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na tuhumar tsohon shugaban bankin da badakaloli akalla 20.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Emefiele ya samu kaso daga kwangilar?
Bayan zargin da hukumar EFCC ta yi wa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele na raba kwangila ga 'yan uwansa, lauyan wanda ake kara Mathew Burkaa SAN ya yi shaidan tambayoyi a gaban kotun.
The Guardian ta wallafa cewa daga cikin abin da Burkaa SAN ya tambaya akwai shin ko kamfanonin da ake zargin na 'yan uwansa ne sun ba Emefiele wani kaso na kudin kwangilar.
Shaidan EFCC, Michael Agboro, ya bayyana cewa a binciken da su ka gudanar, babu shaida cewa kamfanonin sun raba wani kaso na kudin aikin da Emefiele.
Shaidan ya kuma amince da cewa tabbas, Emefiele na da hurumin bayar da kwangila a matsayinsa na shugaban bankin baki daya.
EFCC ta sake maka Emefiele kotu
A wani labarin kun ji cewa hukumar hana yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati (EFCC) ta sake shigar da kara ta na tuhumar tsohon gwamnan EFCC da buga takardun kudi da tsada.
A sabuwar tuhumar, ana zargin Mista Godwin Emefiele ya buga takardun kudi N684m kan kudi N18.96bn, lamarin da EFCC ke yiwa kallon barnatar da kudin kasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng