InnalilLahi: Kashim Shettima Ya Sake Yin Rashi a Rayuwa, Mutuwa Ta Ratsa Gidansa
- Allah ya yiwa surukar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, rasuwa a birnin Kano a ranar Lahadi, 23 ga watan Yunin 2024
- Hajiya Maryam Abubakar Albishir wacce mahaifiya ce ga matar Kashim Shettima, Hajiya Nana Shettima ta rasu ne bayan ta yi fama da doguwar jinya
- Marigayiyar mai shekara 69 a duniya za a yi jana'izarta kamar yadda addinin musulunci ya tanada a ranar Lititin, 24 ga watan Yuni a birnin Kano
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya rasa surukarsa, Hajiya Maryam Abubakar Albishir, wacce ta riga mu gidan gaskiya.
Marigayiyar mai shekara 69 a duniya ta rasu ne a birnin Kano a ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni bayan ta yi fama da doguwar jinya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar, Stanley Nkwocha ya fitar a shafinsa na X a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Surukar Kashim Shettima ta rasu
"Mataimakin shugaban ƙasa ya rasa surukarsa, Hajiya Maryam Abubakar Albishir, wacce ta rasu a Kano da yammacin ranar Lahadi bayan ta yi fama da jinya."
"Za a yi jana'izar Hajiya Maryam, mahaifiyar matar mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima a ranar Litinin da yamma a Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."
- Stanley Nkwocha
Surukar Shettima ta kasance abin koyi
Sanarwar ta bayyana marigayiyar a matsayin uwa abin koyi kuma mai tausayi a cikin al’ummarta sannan Musulma mai kishin addini.
A cikin sanarwar an miƙa saƙon ta'aziyya ga mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, Hajiya Nana Shettima da iyalansu sakamakon wannan babban rashin da suka yi.
Matar mahaifin Kashim Shettima ta rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya rasa matar mahaifinsa, Hajiya Hauwa Abba Kormi, wacce ta riga mu zuwa gidan gaskiya.
Hajiya Hauwa Abba Kormi mai shekara 69 a duniya ta rasu bayan ta yi fama da doguwar jinya a ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairun 2024.
Marigayiyar da aka yi jana'izarta a birnin Maiduguri ta rasu ta bar ƴaƴa biyar, ƴaƴan miji da jikoki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng