Yayin da Alhazai Suka Fara Dawowa Gida, Gwamna Ya Nemi a Binciki Hukumar NAHCON
- Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya nuna takaicinsa kan yadda hukumar NAHCON ta tafiyar da ayyukan Hajjin bana na shekarar 2024
- Gwamna Bago ya yi kira ga majalisar tarayya da ta binciki tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta bayar domin gudanar da aikin Hajjin banaa
- A cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa ya fitar, Gwamna Bago ya nuna takaicinsa kan yadda aka ba Alhazai kuɗin guzuri na Dala 400 duk da sun biya N8m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi kira ga majalisar tarayya da ta binciki tallafin Naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bayar domin gudanar da aikin Hajji na 2024.
Gwamnan ya bayyana ayyukan hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) na wannan shekarar a matsayin gazawa.
Gwamna Bago na so a binciki NAHCON
Gwamna Mohammed Bago ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Akwai buƙatar majalisar tarayya ta binciki tallafin Naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta fitar domin aikin Hajjin 2024."
"Abin takaici ne ace an ba Alhazai dala 400 kacal domin su kula da kansu na tsawon kwanaki 40 duk da biyan Naira Miliyan 8 da kowane mahajjaci ya yi."
"Naira biliyan 90 za ta yi tasiri sosai idan aka raba wa jihohi. Kudaden sun isa a gudanar da kasafin hukumar ilimi na bai ɗaya na tsawon shekaru huɗu."
- Mohammed Umaru Bago
Hajji: Wane kira Gwamna Bago ya yi?
Gwamna Bago ya yi kira da a sake duba dokar da ta kafa hukumar NAHCON, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Gwamnan ya kuma nuna damuwarsa kan yadda hukumar NAHCON ta mayar da kanta mai gudanar da shirye-shiryen ayyukan Hajji maimakon ta zama mai lura da ayyukan.
Gwamna Bago ya bayyana cewa zai jagoranci sauran gwamnoni inda za su tura kuɗiri zuwa ga majalisa ta yadda za a sake duba dokar hukumar NAHCON.
Gwamna Bala ya caccaki NAHCON
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya caccaki hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) kan aikin Hajjin bana na shekarar 2024.
Gwamna Bala ya nuna damuwa kan yadda hukumar ta ba mahajjatan kunya a Saudiyya ganin yadda ta ke tafiyar lamarin aikin Hajjin bana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng