Nasir El Rufai Ya Ziyarci Buhari a Daura, Hotuna Sun Bayyana

Nasir El Rufai Ya Ziyarci Buhari a Daura, Hotuna Sun Bayyana

  • Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
  • Ziyarar da El-Rufai ya kai Daura, mahaifar Buhari na zuwa ne kwana ɗaya bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai irin wannan ziyarar ga tsohon shugaban ƙasan
  • Ziyarar jigon na jam'iyyar APC ga Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin jihar Kaduna ke zargin gwamnatinsa da wawure Naira biliyan 423

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Daura, jihar Katsina - Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Tsohon ministan na babban birnin tarayya Abuja ya ziyarci Buhari ne a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: An yi jana'izar mahaifin sanatan Arewa, Shettima da sanatoci sun halarta

El-Rufai ya ziyarci Buhari a Daura
Nasir El-Rufai ya kai ziyara wajen Buhari a Daura Hoto: @MuyiwaAdekeye
Asali: Twitter

Mai taimakawa tsohon gwamnan kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 23 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin da yasa El-Rufai ya ziyarci Buhari

A cewar sanarwar jigon na jam’iyyar APC ya je ta'aziyya ne ga Lawal Sani Sade, shugaban kamfanin Duke Oil, a Daura.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya kuma ziyarci fadar Sarkin Daura a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyyar ga hamshaƙin ɗan kasuwan.

Ziyarar El-Rufai zuwa Daura na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma tsohon dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya ziyarci Muhammadu Buhari.

Ziyarar ta El-Rufai na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin jihar Kaduna ke zargin gwamnatinsa da karkatar da maƙudan kuɗaɗe.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya bayyana mafita 1 game da rikicin da ya mamaye PDP a Katsina

Tsohon gwamnan na Kaduna dai ya nuna cewa ko kaɗan bai damu da binciken da majalisar dokokin jihar take yi ba a kan gwamnatinsa.

An buƙaci a cafke El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa an gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar Kaduna domin neman a cafke Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Masu zanga-zangar ƙarkashin ƙungiyar KCWGG sun mamaye gidan gwamnati da ke Kaduna, domin neman a binciki tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai tare da kama shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel