Gwamna Ya Dauki Tsattsauran Mataki Kan Masallatai da Coci a Plateau, Ya Kakaba Doka
- Gwamna Caleb Mutfwang ya haramta tare hanyoyi da ake yi yayin ibadar Musulmai ko Kiristoci a fadin jihar baki daya
- Bayan wannan sabon umarni, gwamnan ya kuma bukaci binciken takardun amincewa da gina wuraren ibada daga hukumar JMDB
- Wannan mataki bai rasa nasaba da yawan korafi da jama'a ke yi lokacin ibada a masallatai ko coci da ake rufe hanyoyi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Gwamnatin jihar Plateau ta dauki mataki kan masallatai da coci da ke tare hanyoyi yayin ibada.
Gwamna Caleb Mutfwang shi ya tabbatar da haka inda ya ce ya haramta kange hanyoyi da ake yawan samu a jihar lokacin ibada.
Gwamna ya hana Musulmai, Kirista tare hanyoyi
Daily Trust ta ruwaito cewa Caleb ya kuma bukaci duka wuraren ibada su mika takardun amincewa da hukumar kula da birane (JMDB) ta ba su yayin gina wuraren ibadun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bakin babban manajan hukumar, Hart Bankat.
An rubuta takardun ga kungiyar Kiristoci ta CAN da Jama'atul Nasril Islam (JNI) da ke jagorantar addinan biyu, cewar BusinessDay.
Sakataren kungiyar Jama'atu Nasril Islam, JNI a jihar, Dakta Salim Musa Umar ya tabbatar da samun takardar.
Sanarwar haramta tare hanyoyin ta bukaci shugabannin addinai su gargadi mambobinsu domin bin umarnin yadda ya kamata.
Sanarwar haramta tare hanyoyi a Plateau
"Bayan rattaba hannu a dokar a ranar 1 ga watan Maris 2024, ina mai sanar da ku haramta tare hanyoyi da wuraren ibada ke yi."
"Muna ba da shawarar duka wuraren ibada su samar da isasshen wuri domin ajiye ababan hawa yayin ibada nesa da manyan hanyoyi."
"Duka wuraren ibada za su kawo takardun amince musu yin gini da hukumar JMDB ta ba su domin gudun fuskantaar hukunci."
- Cewar sanarwar
CAN ta hukunta Fasto kan dukan Musulmi
Kun ji cewa Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) reshen jihar Oyo ta roki gafarar al'ummar Musulmai a jihar kan abin da wani Fasto ya yi.
Kungiyar ta yi rokon ne bayan wani Fasto ya farmaki wani magidanci da matansa biyu kan yanka ragon layya.
Asali: Legit.ng