Dakarun Sojojin Sama Sun Yi Nasara Kan Barayin Man Fetur a Najeriya
- Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasarar kai hare-hare a haramtattun wuraren tace man fetur a yankin Kudancin Najeriya
- A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na rundunar ya fitar, ya bayyana cewa an lalata haramtattun wuraren guda 13 da kwale-kwale guda bakwai
- AVM Edward Gabkwet ya kuma bayyana cewa dakarun sojojin za su ci gaba da kai hare-haren har sai an ga bayan masu ɓarna ga tattalin arziƙin ƙasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce dakarunta na Operation Delta Safe sun lalata haramtattun wuraren tace man fetur guda 13 da kwale-kwale bakwai a yankin Kudancin Najeriya.
Dakarun sojojin sun lalata haramtattun wuraren ne a jihohin Rivers, Bayelsa da Imo.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojojin sama, AVM Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Lahadi, a birnin tarayya Abuja, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sojoji suka tarwatsa ɓarayin man fetur
Edward Gabkwet ya ce hare-haren saman da aka kai a tsakanin ranakun 18 ga watan Yuni da 22 ga watan Yuni, sun tarwatsa motocin J-5 guda biyar da ke ƙoƙarin satar man fetur daga tankoki, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin haramtattun wuraren an gano su ne a kusa da kogin Imo a ranar 18 ga watan Yuni, inda aka lalata su yayin da masu satar man suka tsere.
A cewarsa, an kuma kai wasu hare-haren a Wilcourt a jihar Rivers a ranar, 19 ga watan Yuni, a wani haramtaccen wuri inda akwai wani kwale-kwale da ke ɗauke da kayan man fetur.
Edward Gabkwet ya kuma ƙara da cewa dakarun sojojin sun kuma lalata wasu haramtattun wuraren tace man fetur da ke a yankin Tunu cikin jihar Bayelsa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa waɗannan hare-haren za a ci gaba da kaisu har sai an kawo ƙarshen ɓata garin.
Sojojin sama sun hallaka ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta kashe ƴan bindiga sama da 100 a wani samame da ta kai sansanin Kuka Shidda da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.
Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji ne suka yi ruwan wuta kan ƴan bindigar da daddare, wanda bisa nasara suka murƙushe su da yawa.
Asali: Legit.ng