Babba Fasto Ya Yi Martani Bayan Gobara Ta Tafka Barna a Cocinsa

Babba Fasto Ya Yi Martani Bayan Gobara Ta Tafka Barna a Cocinsa

  • Fasto Chris Oyakhilome ya ce za su sake gina ɗakin taro mai kyau, kuma mai ɗaukaka bayan gobarar da ta mamaye hedikwatar cocin Christ Embassy
  • Chris Oyakhilome wanda ya kafa cocin Christ Embassy ya ce babu wani abu da ke faruwa da ɗan Adam bisa kuskure
  • Babban faston ya bayyana cewa duk abin da yake faruwa a rayuwar ɗan Adam an riga da an kammala tsarawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Asese, jihar Ogun - Shugaba kuma wanda ya kafa LoveWorld Incorporated, Fasto Chris Oyakhilome, ya mayar da martani kan gobarar da ta tashi a hedikwatar cocin Christ Embassy da ke unguwar Oregun, a birnin Ikeja na jihar Legas.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga har cikin fadar babban basarake sun tafka barna

Fasto Chris Oyakhilome ya ce cocin za ta gina babban ɗakin taro mai girma, mai kyau, kuma mai ɗaukaka biyo bayan gobarar da ta auku.

Fasto Chris Oyakhilome ya yi magana kan gobara a cocin Christ Embassy
Fasto Chris Oyakhilome ya ce za su sake gina babbar coci Hoto: @Bidemi_Tayo/@Chief_Augustin1
Asali: Twitter

Me Fasto Chris ya ce kan gobarar?

Babban faston ya ce babu abin da yake faruwa ga ɗan Adam bisa kuskure, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana hakan ne a yayin harkokin coci na ranar Lahadi a sansanin cocin, da ke Asese, a jihar Ogun, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

"Babu abin da yake faruwa a rayuwar ɗan Adam bisa kuskure. A lokacin da bam ya tashi a barikin Ikeja a shekarar 2001, ginin ya girgiza sosai ta yadda muka yi zaton zai ruguje."
"Na gayawa kaina cewa idan ya ruguje, zan gina babba wanda yafi na da. A ƙarshe bai ruguje ba sannan muka kira injiniyoyi su duba ko akwai buƙatar a rushe a sake gina wani, amma lafiyarsa ƙalau."

Kara karanta wannan

An shiga ɗimuwa bayan wasu miyagu sun hallaka Birgediya-janar na soja a Abuja

"Yanzu da haka ya faru, za mu gina babba, mafi kyau. Wannan ba shi ba ne abin da muke kira kuskure. Duk abin da yake faruwa a rayuwarmu an riga da an tsara shi."

- Fasto Chris Oyakhilome

Gobara ta tashi a cocin Christ Embassy

A wani labarin kuma, kun ji cewa gobara ta tashi a gadan gadan a hedikwatar cocin Christ Embassy, dake unguwar Oregun birnin Ikeja, babban birnin jihar Legas.

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas sun duƙufa wajen kashe gobarar wacce ta tashi kafin a fara ayyukan ibadah na ranar Lahadi, 23 ga watan Yunin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng