Matsin Rayuwa: Tinubu Ya Shawarci ’Yan Najeriya Kan Yadda Za Su Samu Abinci Cikin Sauki
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shawarci ‘yan Najeriya kan yadda za a shawo kan tsadar kayan abinci a kasar
- Ta bakin hadiminsa, ya ce akwai bukatar kowa ya natsu ya ba da gudunmawa wajen gina kasa, musamman duba da yanayin da ake ciki
- Tun bayan hawan Tinubu mulki ake samun kalubalen ci gaban tattalin arziki da kuma tashin farashin kayayyaki a kasuwanni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta yi kira ga 'yan Najeriya su rungumi noma ido rufe don magance tashin farashin kayan abinci da ake fuskanta a kasar.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ne ya yi wannan kiran yayin taron da ya yi da wata kungiyar editocin yanar gizo ta ACOE a Abuja.
Shugaban kungiyar ACOE, Martins Odiete ne ya fitar da sanarwar bayanan Bayo a taron manema labarai da ya yi a ranar Asabar a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin yadda gwamnati ta taso yaki da yunwa
A cewarsa:
"A shekarar 1976, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da shirin 'Operation Feed the Nation,' don karfafa aikin gona.
"A shekarar 1984, lokacin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki, akwai karancin shinkafa, madara, da sukari, sai gwamnati ta bude gidajen ajiya don samar da wadannan kayan ga jama'a.
"Wannan ba shi ne karon farko da muke fuskantar irin wannan kalubalen ba.
"Gwamnati na zuba jari a harkar noma domin samar da abinci mai araha, kuma a mu na ‘yan kasa, dole mu taka tamu rawar."
Tinubu ya koka kan halin da ake ciki
Mr. Onanuga ya amince cewa abubuwa ba sa tafiya yadda shugaban kasa Bola Tinubu ke so a halin da ake ciki, Daily Nigerian ta tattaro.
Duk da haka, ya tabbatar da cewa a cikin watanni 12 masu zuwa, 'yan Najeriya za su fara ganin sakamakon kokarin da gwamnatin ke yi don amfanin kasar.
Duniya na fuskantar matsalar tsadar rayuwa, inji Tinubu
Ya kara da cewa:
"Kodayake mutane na korafi game da wahala, na fadawa BBC cewa matsalar tsadar rayuwa ta bazu a duniya baki daya.
"Watakila abin da ke faruwa a duniya yanzu wani juyin zamani ne, kuma kasashe dole su shiga wasu wahalhalun.
"Muna cikin wannan yanayi, amma wannan gwamnati na yin kokari matuka wajen rage wahalhalun da jama'armu ke fuskanta."
Mr. Onanuga ya tabbatarwa kungiyar ACOE cewa, za a ci gaba da samun kyakkyawar hulda a tsakani wajen isar da labarai bisa tsarin yadda ake yin su a duniya, rahoton Tribune Online.
Ku koma gona ko yunwa ta kashe ku, Tambuwal
A baya, Aminu Waziri Tambuwal ya taba shawartar mutane kan su koma gona don gudun kada yunwa ta kashe jama'a.
Ya bayyana yadda ya kamata 'yan kasa su yi don tabbatar da ba su kwana da yunwa ba duba da yadda kasar ke ciki.
Shugabanni da masu mulki a Najeriya kan daura laifin rashin abinci ga 'yan kasar da ba sa zuwa gona don neman abinci.
Asali: Legit.ng