Ku koma gona kada yunwa ta kashe ku - Tambuwal ya shawarci mutan Sokoto
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, ya roki manoma da su ci gaba da kara kaimi wajen yin noma domin taimakawa kasar wajen farfado da tattalin arzikinta. Ya ce hakan ne zai sa abinci ya wadatu da gudun mace mace saboda yunwa.
Tambuwal ya bayyana hakan a jihar Sokoto, yana mai nuni da cewa tattalin arzikin kasar na ci gaba da tabarbarewa, fiye da tunanin mutane.
"A don haka, a irin wannan lokacin ne ya kamata mu tashi tsaye, idan har manoma suka ce ba zasu je gona ba, to karshe yunwa za ta kashe 'yan kasar saboda karancin abinci.
"Haka zalika, wadatar abinci na da matukar amfani, wannan ne ya sa gwamnati ke ware taki mai yawa a kowacce shekara tare da saidawa manoma a farashi mai rahusa.
"Muna fatan su manoman zasu yi amfani da takin kamar yadda ya dace, an kuma samar da kayan aikin gona domin ganin anyi noman da zai wadatar da kasar," a cewarsa.
KARANTA WANNAN: Sabbin mutane 304 sun kamu da COVID-19 a Nigeria, Abuja na da 90
A wani labarin; Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu daga shafin hukumar dakile yaduwar cutuka ta Nigeria (NCDC) a Twitter @NCDCGov na nuni da cewa sabbin mutane 304 sun kamu da cutar nan mai hatsari ta COVID-19 a Nigeria.
Kamar yadda kuka saba, Legit.ng Hausa na kawo maku kididdigar mutane da cutar ta kama a kowacce jiha, kamar yadda hukumar NCDC ta ke wallafawa a daren kowacce rana.
Ga jadawalinsabbin mutanen da cutar da kama da jihohinsu:
FCT-90
Lagos-59
Ondo-39
Taraba-18
Rivers-17
Borno-15
Adamawa-12
Oyo-11
Delta-9
Edo-6
Bauchi-4
Kwara-4
Ogun-4
Osun-4
Bayelsa-3
Plateau-3
Niger-3
Nasarawa-2
Kano-1
Mutane 44,433 ke dauke da cutar a halin yanzu, yayin da aka sallami mutane 31,851 daga asibiti bayan warkewarsu daga cutar, sai kuma mutane 910 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng