'Yan Bindiga Sun Shiga Har Cikin Fadar Babban Basarake Sun Tafka Barna

'Yan Bindiga Sun Shiga Har Cikin Fadar Babban Basarake Sun Tafka Barna

  • Ƴan bindiga sun yi yunƙurin sace basaraken ƙauyen Rumu-Elechi da ke ƙaramar hukumar Port Harcourt ta jihar Rivers
  • Miyagun waɗanda ba su yi nasarar sace basaraken ba, sun yi awon gaba da ɗan sandan da ke ba shi kariya da direbansa
  • Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce an tura tawaga ta musamman domin ceto mutanen da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da wani jami’in ƴan sanda da kuma direban da ke aiki tare da wani basarake mai daraja a jihar Rivers.

An yi garkuwa da mutanen ne a ranar Asabar a gidan mai martaba, Cif Cornwell Ihunwo da ke kusa da tsibirin Eagle Island.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan sojojin Najeriya sun hallaka dan sanda

'Yan bindiga sun sace dan sanda a Rivers
'Yan bindiga sun sace dan sandan da ke gadin basarake a Rivers Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Cif Cornwell Ihunwo shine sarkin ƙauyen Rumu-Elechi da ke Nkpolu-Orowurokwo a ƙaramar hukumar Port Harcourt, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai farmaki a fadar basarake

Jaridar Daily Trust ta ce wani babban jami'in ƴan bangan Diobu kuma babban jami'in tsaro na Nkpolu-Orowurokwo, Godstime Ihunwo, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

Godstime ya yi zargin cewa manufar ƴan bindigan ita ce su sace basaraken, inda ya yi Allah wadai da hakan.

"Na samu kira dangane da sace mai martaba Cornwell Ihunwo da misalin ƙarfe 9:00 a ranar Asabar, 22 ga watan Yunin 2024."
"Nan da nan na garzaya zuwa gidansa da ke tsibirin Eagle Island inda na tarar da shi. Cif Cornwell ya sanar min da cewa direbansa da ɗan sandan da ke ba shi kariya ne aka sace."

Kara karanta wannan

An shiga ɗimuwa bayan wasu miyagu sun hallaka Birgediya-janar na soja a Abuja

"Mun yi Allah wadai da shirin sace Cif Cornwell Ihunwo sannan muna kira ga ƴan sanda su tabbatar an gudanar da cikakken bincike a kan lamarin."

- Godstime Ihunwo

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Rivers, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Ta bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar, Olatunji Disu, ya umarci tawagar Octopus Strike Force da su gudanar da bincike kan lamarin tare da tabbatar da cewa sun kuɓutar da mutanen.

Ta kuma ƙara da cewa kwamishinan tare da ƴan tawagarsa sun ziyarci inda lamarin ya auku.

Ƴan bindiga sun kai hari a Katsina

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun sake kai hari kauyen Mai Dabino da ke ƙaramar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

Maharan sun kai farmakin ne da daren ranarAsabar, 22 ga watan Yunin 2024 a ƙauyen inda suka yi ta harbe-harbe sannan suka hallaka mutum bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel