Hajji Mabrur: Jirgin Farko da ya Kwaso Alhazan Najeriya Daga Saudiya ya Iso Gida

Hajji Mabrur: Jirgin Farko da ya Kwaso Alhazan Najeriya Daga Saudiya ya Iso Gida

  • Bayan shafe akalla wata daya a kasa mai tsarki suna gudanar da aikin Hajji, alhazan Najeriya sun fara dawowa gida
  • Jirgin farko na alhazan ya iso gida a ranar Asabar, misalin karfe 9:42 na dare a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi
  • Alhazan sun jinjinawa gwamnati, da ta kula da dawainiyar su yayin gudanar da aikin hajjin na bana tun daga farko har zuwa karshe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kebbi - Kashi na farko na alhazai 410 daga jihar Kebbi da suka yi aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya sun dawo gida, kuma shine jirgin farko na alhazan Najeriya da ya iso gida.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarauta, ƴan bindiga sun kai hari Masallaci, sun sace basarake

Alhazan da suka fito daga kananan hukumomin Arewa da Jega, sun sauka a filin jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi, da misalin karfe 9:42 na yammacin ranar Asabar.

Jirgin farko na alhazan Najeriya na iso gida daga Saudiya
An fara jigilar alhazan Najeriya daga Saudiya zuwa gida. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Twitter

sAlhazan Najeriya sun fara dawowa gida

Mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama'a, Yahya Sarki ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yahya Sarki ya ce:

"Dawowar su ya yi nuni da fara jigilar alhazan Najeriya daga kasa mai tsarki zuwa gida, domin Kebbi ce ta kaddamar da jigilar farko na alhazan zuwa Saudiya wata daya da ya gabata.
"Dukkanin alhazai mata da maza da suka sauka daga cikin jirgin suna cikin koshin lafiya kuma sun nuna cewa sun samu kyakkyawar kulawa yayin gudanar da aikin Hajjin."

Alhazan Kebbi sun jinjinawa Nasir Idris

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane da suka addabi Taraba, sun ba da bayanai

Wata Hajiya Barakah Maishanu ta yi godiya ga Gwamna Nasir Idris wanda ya tabbatar da alhazan jihar sun samu kulawa ta musamman a lokacin da suke Makkah da Madina.

Alhazai da dama sun jinjinawa gwamnan jihar, da ya bayar da umarnin kula da dawainiyar su yayin gudanar da aikin hajjin daga farko har zuwa karshe.

Alhaji Shehu Mu’azu ya mika sakon gaisuwar gwamnan ga ga al’ummar jihar Kebbi bisa goyon bayan da suke ba gwamnatinsa, tare da ba su tabbacin fifita su a kan komai.

An hana alhazai dauko guzurin Zamzam

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanya doka ga mahajjata kan ɗauko ruwan Zamzam daga ƙasa mai tsarki.

Hukumar ta haramtawa mahajjatan ɗauko ruwan Zamzam yayin da suke dawowa gida Najeriya daga Saudiyya bayan kammala aikin Hajji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel