Sarautar Kano: Lauyoyin Arewa Sun Yabawa Hukuncin Kotu, Sun Gargadi Gwamna Abba

Sarautar Kano: Lauyoyin Arewa Sun Yabawa Hukuncin Kotu, Sun Gargadi Gwamna Abba

  • Kungiyar Lauyoyi a Arewacin Najeriya ta shawarci Abba Kabir ya yi biyayya ga hukuncin kotu kan masarautu
  • Kungiyar ta ce wannan hukunci ya tabbatar da bin gaskiya da doka bayan rushe masarautun jihar da Abba ya yi
  • Ta kuma bukaci gwamnan ya ba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero hakuri kan wulakanta shi da ya yi a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar Lauyoyi da ke Arewacin Najeriya (NCNLPIA) ta yi martani kan hukuncin kotu game da masarautun jihar Kano.

Kungiyar ta yabawa hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta mayar da Aminu Ado Bayero kan kujerar sarauta.

Lauyoyi sun yabawa hukuncin kotu a rigimar sarautar Kano
Kungiyar Lauyoyi a Arewa sun gargadi Abba Kabir kan hukuncin sarautar Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf, Masarautar Kano.
Asali: UGC

Kano: Lauyoyi sun yabawa hukuncin kotu

Kara karanta wannan

Bayan yanke hukunci, an yaɗa bidiyon yadda dubban Kanawa suka cika fadar Aminu Ado

Shugaban kungiyar, Napoleon Otache shi ya bayyana haka a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024 a cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Otache ya ce hukunci ya tabbatar da bin doka da oda da kuma kare martabar masarautun.

Ya ce wannan hukunci ya tabbatar da muradun mutanen jihar Kano gaba daya da kuma nuna rashin bin ka'ida na gwamnatin jihar ta yi wurin rusa masarautun.

"Bangaren shari'a ta ankarar da jama'a cewa akwai yadda za a gyara barnar da Majalisar jihar Kano ta yi kan masarautu guda biyar."

- Napoleon Otache

Lauyoyin Arewa sun gargadi gwamnan Kano

Har ila yau, kungiyar ta bukaci Abba Kabir ya ba Aminu Ado Bayero hakuri kan irin cin mutunci da kuma wulakanci da ya yi masa.

Kungiyar ta kuma shawarci Abba Kabir ya tabbatar da yin biyayya ga hukuncin domin samun zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

"Akwai rikitarwa": Farfesan Lauyoyi, Yadudu ya gano kuskure a hukuncin shari'ar sarautar Kano

Ta ce bangaren shari'a kadai ta ragewa talaka wurin yi masa adalci inda ta tabbatar da har yanzu ana bin doka da oda.

Dubban masoya sun tarbi Aminu Ado Bayero

A wani labarin, kun ji cewa a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024 dubban Kanawa sun tarbi Aminu Ado Bayero.

Dandazon jama'ar sun kuma kai gaisuwar Juma'a ga fadar Sarkin a Nassarawa domin nuna masa goyon baya.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rigimar masarautun jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.