'Yan Sanda Sun Aikawa Gwamna Abba Amsar Umarnin Tuge Aminu Ado Daga Fadar Nassarawa
- Kwamishinan ƴan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel ya yi martani kan umarnin fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa
- Gumel ya ce ba za su bi umarnin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba tun da ya shigar da korafi a babbar kotun jihar kan lamarin
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinan ya fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta yi martani kan umarnin Gwamna Abba Kabir kan rushe fadar Nassarawa.
Kwamishinan ƴan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya bayyana dalilin bijirewa umarnin gwamnan na fitar da Aminu Ado Bayero daga fadar.
Ƴan sandan Kano sun bijirewa Abba Kabir
Hussaini Gumel ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Punch ta wayar tarho a yau Juma'a 21 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce babu yadda za su bi umarnin gwamnan bayan ya shigar da korafi a babbar kotun jihar kan fitar da Aminu Ado daga fadar Nassarawa.
Dalilin 'yan sanda na bijirewa Abba
"Ƴan sanda ba za su bi umarnin gwamnan ba kan fitar da Amini Ado daga fada saboda gwamnatin ta shigar da korafi a babbar kotun jihar da za a yi hukunci a ranar Litinin 24 ga watan Yunin 2024."
"Bai kamata mu bi umarnin ba saboda sun shigar da korafi kan lamarin, idan mu ka dauki mataki kaman muna katsalandan ne ga kotun tun da ba mu san menene zai faru ba yayin hukuncin."
- Hussaini Gumel
An jibge jami'an tsaro a fadar Nassarawa
Rahotanni sun tabbatar da an jibge jami'an tsaro a fadar musamman bayan umarnin gwamnan a jihar.
Yayin da kwamishinan ya ki bin umarnin gwamnan, Aminu Ado ya ci gaba da zama a fadar da fadawa da kuma dubban masoyansa.
Kano: Farfesa ya magantu kan hukuncin kotu
A wani labarin, kun ji cewa fitaccen lauya a Najeriya, Farfesa Auwal Yadudu ya magantu kan hukuncin kotu a shari'ar sarautar Kano.
Yadudu ya ce hukuncin da alkalin ya yanke a jiya Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 ya zama daban kuma abin rikitarwa da takaici.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng