"Akwai Rikitarwa": Farfesan Lauyoyi Yadudu Ya Gano Kuskure a Hukuncin Shari'ar Sarautar Kano

"Akwai Rikitarwa": Farfesan Lauyoyi Yadudu Ya Gano Kuskure a Hukuncin Shari'ar Sarautar Kano

  • Yayin da kotu ta yanke hukunci kan rigimar sarautar jihar Kano, lauya kuma Farfesa ya bayyana yadda yake ganin matakin
  • Farfesa Auwal Yadudu ya ce hukuncin kotun abin takaici ne da ba a saba gani na wanda ya bata sunan bangaren shari'a a kasar
  • Wannan na zuwa ne bayan hukuncin kotun Tarayya kan dambarwa game da sarautar Kano tsakanin sarakunan kasar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Fitaccen lauya a Najeriya, Farfesa Auwal Yadudu ya magantu kan hukuncin kotu a shari'ar sarautar Kano.

Auwal Yadudu ya ce hukuncin da alkalin ya yanke a jiya Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 ya zama daban kuma abin rikitarwa da takaici.

Kara karanta wannan

Bayan yanke hukunci, an yaɗa bidiyon yadda dubban Kanawa suka cika fadar Aminu Ado

Lauya ya yi martani kan hukuncin kotu game da sarautar Kano
Lauya kuma Farfesa ya magantu kan hukuncin da kotu ta yi game da sarautar Kano. Hoto: Masarautar Kano, Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Facebook

Kano: Farfesa Yadudu ya kushe hukuncin kotu

Farfesan ya bayyana haka ne a yayin hira da jaridar Daily Trust inda ya ce bai kamata alkalin ya yi irin wannan hukunci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bai dace alkalin kotun da aka karawa girma zuwa Kotun Daukaka Kara ya ɗauki irin wannan mataki kan rigimar sarautar ba.

"Hukuncin akwai rikitarwa" - Farfesa Yadudu

"Ta yaya zaka ce ka jingine matakan da aka dauka bisa doka, kuma kace ba ka son shiga lamarin ingancin dokar da aka yi."
Duk wannan abubuwa za a iya kauce musu, hakan bata sunan bangaren shari'a ne, abin takaici ne kuma hukuncin ya bata sunan alkalin."
"Maganar ko matakin gwamnan ya zo kafin ko bayan umarnin ya danganta ne da hujjoji, ya tabbata daga bayanai dokar ta zo ne daga baya."

Kara karanta wannan

"Yana da ɗaure kai," Falana ya faɗi kuskuren da aka yi a hukuncin shari'ar sarautar Kano

- Farfesa Auwal Yadudu

Gwamnan Kano ya umarci rushe fadar Nassarawa

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya umarci fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nassarawa a jihar.

Gwamnan ya ba da umarnin ne ga kwamishinan ƴan sanda a jihar, Hussaini Gumel domin fara gyara da kuma rushe-rushe a fadar Nassarawa.

Sanarwar na zuwan ne awanni kadan bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rigimar sarautar Kano da ake ciki tsakanin Sanusi II da Aminu Ado Bayero.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel