'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Karamar Hukumar Gwamna, Sun Hallaka Mutum 2

'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Karamar Hukumar Gwamna, Sun Hallaka Mutum 2

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ƙaramar hukumar Wukari ta jihar Taraba inda suka hallaka mutum biyu da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Chinkai a ranar Laraba, 19 ga watan Yunin 2024 inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ƙara da ceqa an ɗauki matakai domin hana sake aukuwar hakan a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Ƴan bindiga na ci gaba da tafka ta'asa a ƙaramar hukumar Wukari ta jihar Taraba.

Hari na baya-bayan nan da suka kai, sun kai shi ne a ƙauyen Chinkai, inda suka hallaka mutum biyu a ranar Laraba, 19 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka matashi bayan ya kai musu kudin fansar N16m a Kaduna

'Yan bindiga sun kai hari a Taraba
'Yan bindiga sun hallaka mutum biyu a jihar Taraba Hoto: @Agbukefas
Asali: Twitter

Harin ƴan bindigan na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani ɓarawo ya hallaka wani matashi ɗan shekara 18 mai sana'ar POS a ƙaramar hukumar Wukari, mahaifar gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai harin Taraba

Shugaban ƙaramar hukumar Wukari, Isma'ila Dauda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai ta WhatsApp, cewar rahoton jaridar Vanguard.

"Ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu a ƙauyen Chinkai a ranar, 19 ga watan Yunin 2024 bayan sun shiga ƙauyen sannan suka fara harbi kan mai uwa da wabi."
"Abin akwai takaici yadda ake farmakar matasanmu. Sai dai, an tura da jami'an sojoji zuwa Chinkai, amma kafin su isa garin, ƴan bindigan sun tsere."

- Isma'ila Dauda

Magajin garin Chinkai, Ezekiel Musa, ya yi kira ga gwamnan jihar da ya tabbatar da an ƙara tura jami'an tsaro zuwa ƙauyen nasu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki, 'yan bindiga sun hallaka Amarya mako 1 tak bayan ɗaura aurenta

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Taraba, DSP Gambo Kwache, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Ta ƙara da cewa an tsaurara matakan tsaro a ƙauyen domin gujewa sake kai hari a nan gaba.

Ƴan bindiga sun hallaka bayin Allah

A wani labarin kuma, kun ji cewa an hallaka mutum shida yayin da wasu da dama kuma aka yi garkuwa da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin Bauda da Chibiya a gundumar Maro da ke ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng