Halin da Ake Ciki a Tudun Biri Watanni 6 Bayan Harin Bom, an Yi Biris da Bayin Allah

Halin da Ake Ciki a Tudun Biri Watanni 6 Bayan Harin Bom, an Yi Biris da Bayin Allah

  • A ranar 3 ga watan Disambar shekarar 2023 rundunar sojin Najeriya ta saki bam bisa kuskure kan masu mutane a Tudun Biri
  • Tun bayan lokacin, gwamnati da daukacin mutane sun yi alkawura da dama domin ganin tallafawa mutanen da harin ya ritsa dasu
  • Sai dai bincike ya nuna cewa har yanzu wasu daga cikin marasa lafiya da harin ya ritsa dasu suna bukatar kulawa ta musamman

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - An yi waiwaye kan al'ummar garin Tudun Biri wata shida bayan harin bom da aka kai garin bisa kuskure.

Harin bom din ya kashe mutane masu yawa tare da jikkata da dama wanda har yanzu suna fama da jinya.

Kara karanta wannan

Tsananin zafi ya yi sanadiyyar rayuka 900, musulmai na cigiyar 'yan uwansu

Tudun Biri
Marasa lafiya na bukatar tallafi a Tudun Biri. Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Wani bincike da jaridar Tribune ta fitar ya nuna cewa har yanzu akwai marasa lafiya da harin ya ritsa da su da ba su samu kulawa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tudun Biri: Marasa lafiya sun koka

Sakataren masarautar Tudun Biri, Idris Haruna ya tabbatar da cewa akwai marasa lafiya da dama da suna cikin mummunan yanayi kuma suna buƙatar taimako.

Idris Haruna ya ce lamari mafi muni shi ne na wata yarinya 'yar shekara 11 mai suna Aisha da take kokarin makancewa saboda rashin magani.

Ya kara da cewa akwai wata yarinya mai shekaru shida da aka yiwa tiyata a ciki har yanzu tana buƙatar kulawa amma babu dama.

An fara cikawa mutanen Tudun Biri alkawura

Har ila yau sakataren ya tabbatar da cewa akwai alkawuran da aka musu da a yanzu haka aikinsu ya fara nisa.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Ya ce akwai alkawarin masallacin Jumu'a da aka yi musu wanda yanzu haka ana ƙoƙarin kammala aikinsa.

Idris Haruna ya ce akwai alkawarin hanya da wurin koyon sana'a da aka musu wanda duk yanzu sun kusa kammala.

An dakile yan bindiga a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun sake kai hari yankin birnin tarayya Abuja, sun yi yunƙurin garkuwa da mutane kimanin 20.

Kwamishinan ƴan sandan FCT da kansa ya jagoranci dakarun ƴan sanda suka kai ɗauki kuma suka yi nasarar dakile harin cikin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng