Soke Naɗin Sanusi II: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani Kan Hukuncin da Kotu Ta Yanke

Soke Naɗin Sanusi II: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani Kan Hukuncin da Kotu Ta Yanke

  • Gwamnatin jihar Kano ta ce hukuncin da babbar kotu ta yanke ya nuna cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano
  • Kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai
  • Barista Haruna Dederi ya yi martani kan hukuncin da Mai shari’a A.M Liman ya yanke game da dokar masarautun Kano ta 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta yi martani kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke a ranar Alhamis game da dokar masarautun jihar ta 2024.

Gwamnatin jihar ta ce hukuncin da Mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya yanke ya nuna cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Hukuncin masarautar Kano ya lasawa bangarorin da ke rikici zuma a baki

Gwamnatin Kano ta yi magana kan hukunci kotu
Gwamnatin Kano ta dage kan cewa Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Kano: Gwamnati ta magantu kan hukuncin kotu

Kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isah Dederi ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnati, inji jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ta umarci ‘yan sandan jihar da su fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga karamar fadar gidan Nassarawa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Dederi ya ce ya kamata a fitar da Bayero daga karamar fadar domin gwamnati ta riga ta kammala shirye-shiryen rushewa da kuma gyara fadar.

"Har yanzu Sanusi II ne sarki" - Gwamnatin Kano

Sanarwar ta ce:

“A bisa hukuncin da kotun ta yanke, babu shakka ta sake tabbatar da ingancin dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da sa hannun gwamnan jihar Kano a ranar 23 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Yaron Sanusi II ya yi martani bayan hukuncin kotu kan dokar masarauta

“Ƙarin ma’anar hukuncin shi ne, duk ayyukan da gwamnati ta yi kafin fitowar umarnin wucin gadi na kotun na nan daram. Haka kuma Muhammadu Sanusi II ne Sarkin Kano."

Ana zaman dari-dari a garin Kano

A wani labarin mun ruwaito cewa an fara zaman ɗari ɗari a Kano jim kadan bayan babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan dokar da ta rusa masarautun jihar.

A hannu daya kuma, an ga wani bidiyo da ya nuna yadda magoya bayan Aminu Bayero ke murna bayan kotun ta rusa nadin da aka yiwa Muhammadu Sanusi II.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.