Sarautar Kano: Abba Ya Ba Kwamishinan ’Yan Sanda Sabon Umarni Kan Fadar Nassarawa
- Gwamnatin jihar Kano ta umarci kwamishinan 'yan sanda ya fitar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado daga fadar Nasarawa
- Abba Kabir Yusuf ya ba da wannan umarni domin fara gyara a wasu bangarori na fadar da ke Kano ba tare da bata lokaci ba
- Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rigimar masarautun jihar da ake ta yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir ya umarci fitar da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga fadar Nasarawa a jihar Kano.
Abba Kabir ya ba da umarnin ne ga kwamishinan 'yan sanda a jihar, Hussaini Gumel inda ya ce zai yi gyara tare da rushe-rushe.
Kano: Umarnin Abba game da fadar Nasarawa
Kwamishinan shari'ar a jihar, Haruna Isa Dederi shi ya fitar da wannan sanarwa yayin ganawa da manema labarai, cewar TVC News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dederi ya ce gwamnatin jihar ta gama shirin rushewa tare da gyara na musamman a katangun fadar da suka mutu, Daily Trust ta tattaro.
"Wannan hukunci na kotu ya tabbatar da dokar Majalisar jihar da Gwamna Abba Kabir ya sanyawa hannu a ranar 23 ga watan Mayun 2024."
"Bayan haka, gwamnatin jihar Kano ta umarci kwamishinan 'yan sanda ya fitar da Aminu Ado inda aka shirya fara gyara a fadar tare da rushe wani bangare na katangar ba tare da bata lokaci ba."
- Haruna Isa Dederi
Masarautun Kano: Kotu ta yi hukunci
Wannan sanarwa na zuwa ne awanni kadan bayan Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan rigimar sarautar Kano.
Kotun ta yi fatali da matakan da matakan da gwamnan jihar ya dauka wajen aiwatar da rushe masarautun.
Yan Najeriya sun yi martani hukuncin kotu
A wani labarin, kun ji cewa bayan hukuncin kotu a yau Alhamis 20 ga watan Yunin 2024 kan dambarwar sarautar Kano.
Kotun yayin hukuncin ta rushe matakin da Gwamna Abba Kabir ya dauka kan soke masarautun jihar guda biyar.
Mutane da dama sun yi martani inda suka bayyana ra'ayoyinsu mabambanta gamed da hukucin da kotun ta yanke.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng