"Saura Kiris a Daina Rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare a Takarda," WAEC

"Saura Kiris a Daina Rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare a Takarda," WAEC

  • Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma (WAEC) ta bayyana shirye-shiryen da ta ke yi na zamanantar da jarrabawarta, a daina rubutawa a takarda
  • Shugaban hukumar da ke lura da Najeriya, Dr. Amos Dangut ne ya sanar da haka a Abeokuta, jihar Ogun yayin zagayen sanya idanu kan yadda ake gudanar da jarrabawar
  • Dr. Dangut ya kara da cewa a hankali za su janye rubuta WAEC a takarda, kuma za su fara da makarantun da ke da na'ura mai kwakwalwa yayin da su ke tuntubar ma'aikatar ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ogun- Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma (WAEC) ta ce sannu a hankali za ta janye rubuta jarrabawarta a takarda.

Kara karanta wannan

Mahara sun dira Jihar Binuwai a babur, an shiga fargaba bayan kashe rayuka

Mai lura da hukumar na kasa, Dr. Amos Dangut ne ya shaida shirin da su ke yi a Abeokuta yayin sanya idanu kan yadda jarrabawar ke gudana a wasu makarantun jihar.

WASSCE
WAEC na shirin daina rubuta jarabawa a takarda Hoto: Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

The Nation ta wallafa cewa za su duba yadda za a rika aika wa da na’urorin zamani zuwa cibiyoyin rubuta jarrabawar da aka amince da su a sassan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Za mu bi zamani a hankali,” WAEC

Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma (WAEC) ta ce ana shirin zamanantar da yadda daliban kasar nan ke rubuta jarrabawar WAEC a fadin Najeriya.

Vanguard News ta wallafa cewa idan shirin hukumar na kai na’urorin zamani wuraren zana jarrabawar ya tabbata, ana kyautata zaton daina amfani da takarda baki daya.

Yadda WAEC za ta janye takardu a jarrabawa

Mai lura da hukumar na kasa, Dr. Amos Dangut ya ce amma a hankali za a dauki matakin, inda za a fara ba makarantun da ke da na’ura mai kwakwalwa dama su rubuta jarrabawar a kan na'urorin.

Kara karanta wannan

Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu ya saduda, ya nemi ayi sulhu da gwamnati

Makarantun da ba su da na’urorin kuma za su yi amfani da takarda da biro yadda aka saba, yayin da za su ci gaba da tuntubar ma’aikatar ilimin Najeriya kan lamarin.

WAEC ta hana sakamakon dalibai

A baya mun ruwaito cewa hukumar shirya jarrabawar kammala sakandare ta Afrika ta yamma (WAEC) ta rike sakamakon wasu dalibai da ake zargin sun yi amfani da fasahar AI.

Shugaban hukumar a Ghana, John Kapi ya ce an rike sakamakon dalibai daga makarantu 235 bayan an gano sun yi amfani da fasahar wajen amsa tambayoyin jarrabawar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.