Hankula Sun Tashi Yayin da Wani Soja Ya Hallaka Farar Hula a Abuja

Hankula Sun Tashi Yayin da Wani Soja Ya Hallaka Farar Hula a Abuja

  • An shiga jimami bayan wani sojan Najeriya ya hallaka wani farar hula a birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 20 ga watan Yunin 2024
  • Sojan dai ya hallaka bakaniken ne bayan ya ɗaba wuƙa a kasuwa lokacin da gardama ta ɓarke a tsakaninsu
  • Lamarin ya jawo hargitsi a kasuwar inda mutane suka kulle shagunansu, yayin da ƴan sanda suka garzaya wajen domin dawo da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ana zargin wani soja da ba a tantance kowane ne ba ya daɓawa wani bakanike wuka har lahira a birnin tarayya Abuja.

Sojan dai ya aikata wannan aika-aikar ne a ƙauyen Kugbo da ke kan hanyar Keffi zuwa birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

Soja ya hallaka farar hula a Abuja
Soja ya hallaka bakanike a Abuja Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa sojan ya daɓawa bakaniken wuƙa ne a ranar Alhamis a lokacin da suke gardama, sannan daga bisani ya ranta ana kare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda soja ya kashe bakanike a Abuja

Wani bakanike a yankin mai suna, Yusuf Mustapha, ya shaidawa jaridar Daily Trust ta wayar tarho cewa lamarin ya haifar da rikici a yankin.

Ya bayyana cewa rikicin ya jawo masu masu kanikanci da masu sayar da kayan gyara suka rufe shagunansu.

Yusuf Mustapha ya ce ƴan sanda sun garzaya wurin domin dawo da zaman lafiya.

"Sojan ya zo ne da bakanikensa domin siyan kayan gyaran mota a kasuwar a ranar Alhamis. Ana cikin haka sai gardama ta ɓarke tsakaninsa da wani bakanike a kasuwar. Sojan sai ya ƙwada masa wani abu a kansa."
"Daga nan sai sojan ya zaro wuƙa. Wani bakaniken ya yi ƙoƙarin hana shi yin amfani da ita. Daga nan sai ya shaƙo bakaniken ya ɗaba masa ita har ya mutu. Ganin abin da ya aikata, sai ya ranta a na. kare. Suna can suna nemansa."

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Alhazai 600 ƴan ƙasa 1 sun mutu a Saudiyya, an gano silar ajalinsu

- Yusuf Mustapha

Sojoji sun cafke ɗan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta sanar da kama ɗan ta'addar da ya fitini yankuna da dama a jihar Taraba da ke yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar ta ce ta kama ɗan ta'addan mai Suna Ibrahim Hassan ne yayin da yake ƙoƙarin tserewa bayan sun kai hari kan wasu mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel