Sanusi II vs Aminu: An Fara Zaman Ɗari Ɗari a Kano Bayan Hukuncin da Kotu Ta Yanke

Sanusi II vs Aminu: An Fara Zaman Ɗari Ɗari a Kano Bayan Hukuncin da Kotu Ta Yanke

  • An fara zaman ɗari ɗari a Kano jim kadan bayan babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan dokar da ta rusa masarautun jihar
  • Babbar kotun tarayyar ta tabbatar da dokar rusa masarautun amma ta yi fatali da matakan da aka bi wajen nada sabon sarki
  • A hannu daya kuma, an ga wani bidiyo da ya nuna yadda magoya bayan Aminu Bayero ke murnabayan hukuncin kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Rahotanni sun bayyana cewa an fara zaman ɗari ɗari a Kano bayan hukuncin babbar kotun tarayya na ranar Alhamis kan dokar rusa masarautun jihar.

A zaman kotun na yau, Mai Shari'a Abdullahi Liman ya yi fatali da matakan da gwamnan Kano, Abba Yusuf ya dauka na tsige Aminu Bayero daga sarauta.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano: Kotu ta soke nadin da aka yiwa Sanusi II? Ga karin haske kan hukuncin

Kotu ta yi hukunci kan dokar da ta rusa masarautun Kano
Halin da ake ciki a Kano bayan kotu ta rusa nadin da aka yi wa Muhammadu Sanusi II. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa yanayin birnin na Kano ya sauya bayan kotun ta kuma tabbatar da cewa dokar da ta soke masarautun na nan daram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masoyan Aminu Bayero na murna a Kano

Kamar yadda rahoton ya nuna, an ga magoya bayan Sarkin Kano na 15, sun yi dafifi a gidan Sarkin na Nasarawa inda su ke murnar hukuncin da kotun ta yanke.

Wani bidiyo da wani @tudunwada_mi ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna yadda dandazon jama'a ke maraba da Aminu Babba Dan-Agundi (Sarkin Dawaki Babba).

A wasu ɓangarori na jihar Kano kuwa, an ruwaito cewa mutane na taruwa gungu gungu suna tattaunawa kan hukuncin kotun da ya ba Aminu Bayero nasara.

Abin da hukuncin kotun ya kunsa

Tun da fari, mun ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke da zama a Kano ta tabbatar da dokar da ta rusa masarautu biyar na jihar wanda Abba Yusuf ya zartar.

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan dambarwar masarautar Kano

Kotun ta kuma soke nadin da gwamnatin Kano ta yiwa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano saboda ya biyo bayan umarnin farko da kotun ta bayar na dakatar da nadin.

Hukuncin dai ya haifar da wani nakasu a masarautar Kano, duk da cewa har yanzu Sanusi II ne sarkin Kano, amma za a ci gaba da fafata shari'a kan masarautar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel