Sarkin Kano: Kotu Ta Soke Nadin da Aka Yiwa Sanusi II? Ga Karin Haske Kan Hukuncin

Sarkin Kano: Kotu Ta Soke Nadin da Aka Yiwa Sanusi II? Ga Karin Haske Kan Hukuncin

  • Kai tsaye, babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta rusa nadin da aka yiwa Muhammadu Sanusi II matsayin sarki
  • Mai shari’a Abdullahi Liman ya ce dokar masarautar Kano ta 2024 wanda ta rusa masarautun jihar guda biyar na na daram
  • Sai dai alkalin ya yi fatali da matakan da gwamnan Kano, Abba Yusuf ya dauka wajen aiwatar da dokar rusa masarautun

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayyana cewa dokar masarautar Kano ta 2024 wadda ta rusa masarautun jihar guda biyar na na daram.

Amma kotun ta yi fatali da duk wani mataki da gwamnan Kano, Abba Yusuf ya dauka wajen aiwatar da dokar rusa masarautun jihar.

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan dambarwar masarautar Kano

Kotu ta yi hukunci kan dokar masarautar Kano ta 2024
Kotu ta yi fatali da matakan da gwamnan Kano ya dauka wajen aiwatar da dokar rusa masarautu. Hoto: @masarautarkano, @AKabirbayero
Asali: Facebook

Kotu ta soki matakan gwamnan Kano

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito Mai shari’a Abdullahi Liman ya ce Gwamna Abba Yusuf ya yi biris da umarnin hana mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari’a Abdullahi Liman ya ce duk da mai girma Abba bai karbi takardar umarnin a hannu ba, amma shi (gwamnan) ya amince cewa yana sane da umarnin.

Alkalin kotun ya ce ba daidai ba ne ba gwamnan ya yi watsi da bayanan umarnin kotun wanda aka yada a shafukan sada zumunta.

Abin da hukuncin kotun ya kunsa

1. Kotu ta ji koken majalisar Kano

Kamar yadda babban mataimaki na musamman ga gwamnan Kano a kan sababbin kafofin watsa labarai, Hassan Sani Tukur ya wallafa a X, kotun ta karbi bukatar majalisar Kano.

Kotun ta karbi korafin majalisar da na Antoni Janar na Kano kan dakatar da bukatar rusa dokar da majalisar ta zartar na sabunta dokar masarautun jihar.

Kara karanta wannan

Rigimar masarautar Kano: Babban lauya ya fito da kuskuren kotun da ta ba Bayero nasara

2. Dokar da ta rusa masarautu na nan

Dokar masarautar Kano ta 2024 da ta rusa masarautun jihar guda biyar ta na nan amma kotu ta yi fatali da dukkanin matakan da gwamnan ya dauka wajen aiwatarwa.

3. Sauya kotun da za ta saurari shari'ar

Mai shari'a ya ba majalisa da gwamnatin jihar damar ci gaba da shari’ar kuma ya mayar da karar zuwa kotun Amobeda saboda karin matsayi da ya samu zuwa kotun daukaka kara.

Kotu ta soke nadin Sanusi II?

Bisa ga wannan hukunci da kotun ta yanke, an soke nadin Sanusi II saboda ya biyo bayan umarnin da kotun ta bayar kuma alkalin na ganin an ci mutuncin kotu.

A halin yanzu dai babu Sarki a kan kujerar masarautar Kano, tun da dokar da ta rusa sarautar Aminu na nan, kuma kotu ta soke nadin da aka yi wa Sanusi II.

Kotu ta hana a wulakanta Sanusi II

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar ƴan sanda ta yi martani kan zargin Kwankwaso na sanya dokar ta ɓaci

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jihar Kano ta hana jami'an tsaro na ƴan sanda, sojoji da sauran jami'an tsaro fitar da Muhammadu Sanusi II daga cikin fadar sarki.

Kotun ta kuma hana jami'an tsaron yin duk wani abu da zai wulakanta Sanusi II har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar da sarkin da masu nadin sarki suka shigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel