Kotu Ta Rusa Dokar Ƙarin Ƙananan Hukumomi 33 da Tsohon Gwamna Ya Ƙirƙira

Kotu Ta Rusa Dokar Ƙarin Ƙananan Hukumomi 33 da Tsohon Gwamna Ya Ƙirƙira

  • Rahotanni sun bayyana cewa wata babbar kotu ta rusa dokar da ta kirkiri karin kananan hukumomi 33 a jihar Ondo
  • A watan Satumbar 2023, marigayi Rotimi Akeredolu, tsohon gwamnan Ondo, ya sanya hannu kan dokar bayan amincewar majalisa
  • Alkalin kotun, Adegboyega Adebusoye, ya ayyana kirkirar kananan hukumomin a matsayin abin da ya sabawa kundin tsarin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Ondo - Wata babbar kotun jihar Ondo da ke zama a Akure ta rusa dokar da tsohon Gwamna Marigayi Oluwarotimi Akeredolu ya zartar na kirkirar karin kananan hukumomi 33 a jihar.

Alkalin kotun, Adegboyega Adebusoye, ya yanke wannan hukuncin a ranar Alhamis.

Kotu ta rusa dokar da Akeredolu ya yi a Ondo
Ondo: Kotu ta rusa dokar karin kananan hukumomi. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Asali: Twitter

Adegboyega Adebusoye ya ayyana kirkirar kananan hukumomin a matsayin abin da ya sabawa kundin tsarin mulki kuma ya sabawa ka’ida, in ji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Annoba ta bulla Legas, ta kama sama da mutum 400 bayan kashe wasu da dama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Ondo ya kirkiri kananan hukumomi 33

Majalisar dokokin jihar Ondo ta amince da kudurin samar da karin kananan hukumomin 33 a ranar 15 ga watan Agusta, 2023, bayan ya tsallake karatu na uku.

A watan Satumbar 2023, marigayi Rotimi Akeredolu, tsohon gwamnan Ondo, ya sanya hannu kan dokar kwana daya bayan dawowarsa daga hutun jinya na watanni uku.

Jaridar The Cable ta ruwaito an tsara kananan hukumomi 33 su zama kari ga kananan hukumomi 18, wanda ya kawo adadin kananan hukumomin jihar zuwa 51.

Mutuwar Akeredolu da nada gwamna Aiyedatiwa

Akeredolu ya mutu ne a ranar 27 ga Disamba, 2023, bayan ya dade yana fama da cutar kansa, a karshe ya cika a Turai.

Mun ruwaito cewa an rantsar da Lucky Aiyedatiwa, mataimakin Akeredolu domin ya gaji marigayin.

APC na neman a kama Sanata Kwankwaso

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, fitaccen Sarki mai daraja ya riga mu gidan gaskiya a Landan

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta yi kira ga jami'an tsaron Najeriya da su gaggauta kama tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya zargi Rabiu Kwankwaso da furta kalaman kazafi ga gwamnatin tarayya, abin da ya sa ya nemi a kama tsohon gwamnan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.