Gwamna Fubara Ya Dauki Mataki Yayin da 'Yan Sanda Suka Hana Ciyamomi Shiga Ofis

Gwamna Fubara Ya Dauki Mataki Yayin da 'Yan Sanda Suka Hana Ciyamomi Shiga Ofis

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya ba da sabon umarni ga shugabannin riƙo na kananan hukumomi 23 na jihar Rivers
  • Fubara ya ce sababbin shugabannin riƙon na ƙananan hukumomi da aka rantsar za su iya aiki daga ko ina bayan ƴan sanda sun rufe sakatariyoyi
  • Rundunar ƴan sanda ta rufe ɗaukacin sakatariyoyin bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Gwamna Fubara da Nyesom Wike

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya ce shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 23 za su iya gudanar da ayyukansu daga ko’ina.

Gwamna Fubara ya yanke wannan shawarar ne bayan da ƴan sanda suka kulle sakatariyoyin ƙananan hukumomin tare da jibge jami'an tsaro a ranar Talata, 18 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana yayin da kotu ke shirin sanar da halataccen Sarkin Kano

Gwamna Fubara ya ce ciyamomi su yi aiki daga ko'ina
Gwamna Fubara ya umarci sababbin ciyamomi su yi aiki daga ko'ina Hoto: @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Me Fubara ya gayawa ciyamomin?

Tashar Channels tv ta ce gwamnan ya bayyana haka ne bayan rantsar da sababbin shugabannin riƙon domin maye gurbin tsofafin shugabannin da ke biyayya ga Nyesom Wike a ranar Laraba, 19 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk abin da ya faru jiya (Talata), na sani kuma duniya ta san ba daga gare ku ba ne. Wasu mutane ne suka haddasa shi. Domin haka kada mu bari su ci gaba da ɓatawa jiharmu suna."
"Saboda haka idan kun koma, idan akwai wata matsala ku zama masu bin doka. Ba na son wata rigima. A yanzu za ku iya yin aiki daga ko ina. Abu mafi muhimmanci shi ne daga yau iko na hannunku."

- Siminalayi Fubara

Meyasa ƴan sanda suka kulle sakatariyoyin?

Rundunar ƴan sandan jihar ta ce ta ɗauki matakin kulle sakatariyoyin ne domin hana ci gaba da yiwa doka karan tsaye, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

"Dole ku amayar da abin da kuka ci": Gwamna ya juyo kan ciyamomi 23 da ya kora

A yayin hargitsin da aka yi dai tsakanin magoya bayan Nyesom Wike da Gwamna Fubara an hallaka ɗan sanda ɗaya da ɗan banga mutum ɗaya.

Fubara ya ba da sabon umarni

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya umarci fara binciken tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomin jihar da wa'adinsu ya ƙare.

Gwamna Fubara ya ba mai binciken kuɗi a jihar umarnin ne domin tabbatar da binciken yadda suka gudanar da mulkinsu a ƙananan hukumomi 23.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng