Fargaba Yayin da Kotun Tarayya Za Ta Yanke Hukunci Kan Halaccin Tsige Sarkin Kano
- An fara shiga fargaba a Kano yayin da Babbar Kotun Tarayya ke shirin yanke hukunci kan halaccin dokar da ta dawo da Muhammadu Sanusi II
- A yau Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024 mai shari'a Muhammad Liman zai yanke hukunci a karar da Aminu Babba Ɗanagundi ya shigar
- Mai karar ya nemi kotun ta soke dokar masarautar Kano, sannan ta dawo da Sarki na 15 Aminu Ado da sauran sarakuna huɗu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya mai zama a jihar Kano ta shirya yanke hukunci kan sabuwar dokar masarauta da ta dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II.
Kotun karkashin jagorancin mai shari'a Muhammad Liman ta tsara yanke hukunci kan rigimar sarautar Kano a yau Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024.
Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba DanAgundi ne ya shigar da ƙarar gaban kotun yana ƙalubalantar tube Sarki na 15, Aminu Ado Bayero, Leadership ta ruwaito.
Tun da fari dai kotun ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙorafin take haƙƙin Mai Martaba Sarki Aminu Ado Bayero.
Waɗanda ake tuhuma a shari'ar sarautar Kano
Waɗanda ake ƙara a shari'ar sun haɗa ɗa gwamnatin Kano, majalisar dokoki, kakakin majalisar dokoki da Antoni-Janar wanda shi ne kwamishinan shari'a na Kano.
Sauran su ne kwamishinan ƴan sandan jiha, sufeta janar na kasa (IGP), hukumar tsaron fararen hula NSCDC da hukumar DSS.
A zamanta na karshe, Babbar Kotun Tarayya ta saurari jawaban kowane ɓangare kana ta sanya yau 20 ga watan Yuni a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan halascin rusa masarautu.
Gwamnan Kano ya maido Muhammadu Sanusi II
Idan za ku iya tunawa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Muhammadu Sanusi II kan kargar sarauta bayan rusa masarautu biyar.
Hakan ta faru ne biyo bayan rattaba hannu kan dokar da ta tsige sarakunan da Abdullahi Ganduje ya naɗa tare da dawo da tsarin Sarki ɗaya a jihar Kano.
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, wanda shi ne sarki a lokacin da aka yiwa dokar kwaskwarima, ya kalubalanci matakin da gwamnan jihar ya dauka.
APC ta buƙaci a kama Kwankwaso
A wani rahoton kun ji cewa Jam’iyyar APC ta nemi jami'an tsaro a Najeriya da su gaggauta cafke tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya zargi Rabiu Kwankwaso da furta kalaman kazafi ga gwamnatin tarayya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng